Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَبْلَ وَفَاتِهِ بِثَلَاثٍ يَقُولُ: «لَا يَمُوتَنَّ أَحَدُكُمْ إِلَّا وَهُوَ يُحْسِنُ بِاللهِ الظَّنَّ».
Fassara
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin wafatinsa da (kwana) uku yana cewa: "Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da musulmi cewa kar ya mutu sai shi yana kyautatawa Allah zato da rinjayarwarsa ɓangaren ƙauna a lokacin mutuwa da cewa Allah Zai yi masa rahama kuma Zai yi masa rangwame, domin cewa tsoro abin nema ne dan kyautata aiki, wancan halin ba halin ayyuka ba ne, abin nema a cikinsu (shi ne) rinjayar ƙauna.
Fa'idoji
- Kwaɗayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan shiryarwar al'ummarsa, da tsananin tausayinsa da ita a dukkan halayenta; har a cikin rashin lafiyar rasuwarsa yana yi wa al'ummarsa nasiha kuma yana shiryar da ita akan hanyoyin tsira.
- Al-Ɗaibi ya ce: Ku kyautata ayyukanku a yanzu har zatanku ga Allah ya kyautatu a lokacin mutuwa, domin cewa wanda ya munana aikinsa kafin mutuwa zatansa zai munana a lokacin mutuwa.
- Mafi cikar halaye ga bawa (shi ne) daidaituwar ƙauna da tsoro, da kuma rinjayar so; soyayya ita ce abar hawa, ƙauna kuma mai korowa ce, tsoro kuwa mai tuƙawa ne, Allah kuma Mai sadarwa ne da baiwarSa da kuma karamcinSa.
- Yana kamata ga wanda ya kasance makusanci daga wanda mutuwa ta halarto masa ya rinjayar da ɓangaren ƙauna da kyautatawa Allah zato, a cikin wannan hadisin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi haka kafin ya rasu da (kwana) uku.
Sharhi: العربية
حَثَّ النبيُّ صلى الله عليه وسلم المسلمَ بأن لا يموت إلا وهو يُحسِنُ الظنَّ بالله بتَغْلِيْبِه جانبَ الرجاء عند الاحتضار بأن الله يرحمُه ويعفو عنه، لأن الخوف مطلوب لتحسين العمل، وتلك الحالة ليست حالة الأعمال، فالمطلوب فيها غَلَبَةُ الرجاء.
- حِرْص النبيِّ صلى الله عليه وسلم على إرشاد أمته، وشدة رأفته بها في جميع أحواله؛ حتى في مرض موته ينصح أمتَه ويدلُّها على مسالك النجاة.
- قال الطيبي: أحسنوا أعمالكم الآن حتى يَحْسُنَ ظنُّكم بالله عند الموت، فإنَّ مَن ساء عملُه قبل الموت يَسوء ظنُّه عند الموت.
- أكمل الأَحْوال للعبد اعْتدال الرَّجاء والخوف، وغلبةُ الحب؛ فالمحبَّة هي المرْكَبُ، والرَّجاء حادٍ، والخوف سائق، والله الموصل بمنِّه وكرمه.
- ينبغي على من كان قريبًا ممن حَضَرَه الموت أنْ يُغَلِّب عنده جانب الرجاء وحسن الظن بالله، ففي هذا الحديث أنه صلى الله عليه وسلم قال ذلك قبل أن يموت بثلاث.