Hadisai

Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: أَلَسْتُمْ فِي طَعَامٍ وَشَرَابٍ مَا شِئْتُمْ؟ لَقَدْ رَأَيْتُ نَبِيَّكُمْ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَا يَجِدُ مِنَ الدَّقَلِ مَا يَمْلَأُ بِهِ بَطْنَهُ.

Fassara

Daga Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce: Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba.

Sharhi

Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - yana ambatawa mutane abinda suke a cikinsa na ni'ima, kuma su basu gushe ba suna yadda suke so a cikin abin cin da abin sha, sannan ya bada labarin halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi bai kasance yana samun dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi saboda yunwa ba.

Fa'idoji

  • Bayanin halin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa na gudun duniya.
  • Kwaɗaitarwa akan gudun duniya da kuma ƙarantuwa daga gareta da kuma koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Tunatar da mutane ni'imomin da suke a cikinsu da kuma kwaɗaitarwa akan godewa Allah a kansu.
Sharhi: العربية

يذكر النعمان بن بشير رضي الله عنهما الناس ما هم فيه من نعمة، وأنهم ما زالوا في طعام وشراب مقدار ما شاءوا، ثم أخبر عن حال النبي صلى الله عليه وسلم وأنه ما كان يجد من التمر الرديء ما يملأ به بطنه من الجوع.

  • بيان ما كانت عليه حال النبي عليه الصلاة والسلام من الزهد.
  • الحث على الزهد في الدنيا والتقلل منها والاقتداء بالنبي صلى الله عليه وسلم.
  • تذكير الناس بالنعم التي هم فيها والحث على شكر الله عليها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari