Hadisai

Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ النَّوَّاسِ بْنِ سِمْعَانَ الْأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه قَالَ: سَأَلْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْبِرِّ وَالْإِثْمِ، فَقَالَ: «الْبِرُّ حُسْنُ الْخُلُقِ، وَالْإِثْمُ مَا حَاكَ فِي صَدْرِكَ، وَكَرِهْتَ أَنْ يَطَّلِعَ عَلَيْهِ النَّاسُ».

Fassara

Daga Nawwas ɗan Sam'an alAnsari - Allah Ya yarda da shi ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga aikin alheri da kuma zunubi, sai ya ce: "Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa".

Sharhi

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikin alheri da zunubi, sai ya ce: Mafi girman ɗabi'un aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a tare da Allah da tsoron Allah, da kuma halitta, tare da halitta da jure wa cuta, da ƙarancin fushi, da shinfiɗa fuska, da daddaɗan zance, da sadarwa da ɗa'a da tausayi da kuɓutarwa da kyakkyawar mu'amala da abokantaka. Amma zunubi abinda ya motsu a cikin zuciya na abubuwa masu rikitarwa kuma ya yi kai kawo ba tare da ƙirji ya buɗe gare shi ba, kuma kokwanto ya faru daga gare shi, da tsoron kasancewarsa zunubi, baka so ka bayyanar da shi ba, dan kasancewarsa mummuna ga idanuwa da mutanen kirki da cikakkunsu, hakan domin cewa rai da ɗabi'arta ƙarƙashin tsinkayen mutane akan alherinta, idan ka ƙi tsinkaye akan sashin ayyukanta to shi zunubi ne babu alheri a cikinsa.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan kyawawan ɗabi'u; domin kyawawan ɗabi'u suna daga mafi girman ɗabi'un aikin alheri.
  • Gaskiya da ƙarya al'amarinsu ba ya rikitarwa ga mumini, kai yana sanin gaskiya da hasken da ke cikin zuciyarsa, kuma yana gujewa ƙarya sai ya yi musunta.
  • Daga alamomin zunubi kaikawon zuciya, da ƙin tsinkayar mutane a kansa.
  • Sindi ya ce: Wannan a abubuwa masu rikitarwa ne waɗanda mutane ba sa sanin hakikanin ɗayan ɓangarori biyun daga cikinsu; inba haka ba abin umarni da shi acikin shari'a ba tare da bayyanar dalili a cikinsa ba akan saɓanin hakan daga aikin alheri, abin hanawa daga gare shi kamar hakan, babu buƙatuwa a cikinsu zuwa neman bada fatawar zuciya da kuma nutsuwarta.
  • Wandanda akewa magana a cikin hadisin (su ne) ma'abota nagartacciyar ɗabi'a, ba ma'abota karkatattun zukata ba waɗanda ba sa sanin aikin alheri kuma ba sa ƙin abin ƙi sai dai abinda aka cakuɗa daga son ransu kawai.
  • Ɗibi ya ce: An ce an fassara al-Birr a cikin hadisin da ma'anoni da yawa, ya fassara shi a wani wuri da abinda ransa ya nutsu kuma zuciyarsa ta nutsu da shi, kuma ya fassara shi a wani wurin daban da imani, a wani wurin kuma da abinda zai kusantoka zuwa ga Allah, a nan da kyakkyawar ɗabi'a, an fassara kyakkyawar ɗabi'a: Da jurewa cuta da ƙarancin fushi da shinfiɗar fuska da daddaɗan zance, dukkansu masu kusantar junane a ma'ana.
Sharhi: العربية

سُئِلَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن البر والإثم، فقال: أعظم خِصَال البر حسن الخُلُق مع الله بالتقوى، ومع الخَلْق باحتمال الأذى، وقِلَّة الغَضب، وبسط الوجه، وطيب الكلام، والصلة والطاعة واللطف والمَبَرّة وحسن العشرة والصحبة. وأما الإثم فما تَحَرَّك في النفس مِن المشتبهات وتردَّد دون أنْ ينشرح الصدر له، وحصل في القلب منه الشك، والخوف من كونه ذنبًا، ولم تُرِد أن تُظْهِرَه لكونه قبيحًا لأعيان وأماثل الناس وكُمَّلِهم، وذلك لأن النفس بطبعها تحب اطلاع الناس على خيرها، فإذا كَرِهَت الاطلاع على بعض أفعالها فهو إثم لا خير فيه.

  • الحثُّ على مكارم الأخلاق؛ لأنّ حسن الخلق من أعظم خصال البر.
  • الحق والباطل لا يلتبس أمرُهما على المؤمن، بل يعرف الحق بالنور الذي في قلبه، وينفر عن الباطل فينكره.
  • من علامات الإثم قلق القلب واضطرابه، وكراهة اطلاع الناس عليه.
  • قال السندي: هذا في المشتبهات من الأمور التي لا يعلم الناس فيها بتعيين أحد الطرفين؛ وإلا فالمأمور به في الشرع من غير ظهور دليل فيه على خلاف ذلك من البر، والمنهي عنه كذلك من الإثم، ولا حاجة فيهما إلى استفتاء القلب وطمأنينته.
  • المخاطَب في الحديث أصحاب الفطرة السليمة، لا أصحاب القلوب المنكوسة التي لا تعرف معروفًا ولا تنكر منكرًا إلا ما أُشرِبتْ من هواها.
  • قال الطيبي: قيل فُسِّرَ البر في الحديث بمعان شتى، ففسَّره في موضع بما اطمأنت إليه النفس واطمأن إليه القلب، وفسره في موضع بالإيمان، وفي موضع بما يقربك إلى الله، وهنا بحسن الخلق، وفسر حسن الخلق: باحتمال الأذى وقلة الغضب وبسط الوجه وطيب الكلام، وكلها متقاربة في المعنى.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari