Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي الله عنه: أَنَّ نَاسًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالُوا لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: يَا رَسُولَ اللهِ، ذَهَبَ أَهْلُ الدُّثُورِ بِالْأُجُورِ، يُصَلُّونَ كَمَا نُصَلِّي، وَيَصُومُونَ كَمَا نَصُومُ، وَيَتَصَدَّقُونَ بِفُضُولِ أَمْوَالِهِمْ، قَالَ: «أَوَلَيْسَ قَدْ جَعَلَ اللهُ لَكُمْ مَا تَصَّدَّقُونَ؟ إِنَّ بِكُلِّ تَسْبِيحَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَكْبِيرَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَحْمِيدَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَهْلِيلَةٍ صَدَقَةً، وَأَمْرٌ بِالْمَعْرُوفِ صَدَقَةٌ، وَنَهْيٌ عَنْ مُنْكَرٍ صَدَقَةٌ، وَفِي بُضْعِ أَحَدِكُمْ صَدَقَةٌ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، أَيَأتِي أَحَدُنَا شَهْوَتَهُ وَيَكُونُ لَهُ فِيهَا أَجْرٌ؟ قَالَ: «أَرَأَيْتُمْ لَوْ وَضَعَهَا فِي حَرَامٍ أَكَانَ عَلَيْهِ فِيهَا وِزْرٌ؟ فَكَذَلِكَ إِذَا وَضَعَهَا فِي الْحَلَالِ كَانَ لَهُ أَجْرٌ».
Fassara
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya Manzon Allah, masu dukiyoyi sun tafi da ladaddaki, suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, suna azimi kamar yadda muke yin azumi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, ya ce: "Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne", Suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama yana da lada a cikinta? ya ce: "Shin kuna ganin da ace zai sanyata a cikin haram shin zai zama a kansa akwai zunubi a cikinsa? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada".
Sharhi
Wasu daga talakawa cikin sahabbai sun kawo kukan halinsu da talaucinsu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rashin sadakarsu da dukiyoyi dan su samu lada mai yawa kamar yadda 'yan uwansu masu dukiya da yawa suka samu kuma dan su aikata alheri kamar su; inda cewa su (masu Hali) suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, kuma suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, mu kuma ba ma yin sadaka! Sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da su akan abinda suke da iko akansa na sadakoki, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin yanzu Allah Bai zamo Ya sanya muku abinda zaku dinga sadaka da shi ba akan kanku?! domin cewa faɗinku: Subhanallah, (Tsarki ya tabbata ga Allah) zai zama ladan sadaka gareku, haka nan faɗin: Allahu Akbar, (Allah ne Mafi girma) sadaka ne, da faɗin: La’ilaha illallahu, (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) sadaka ne, da (Horo da aikin alheri) sadaka ne, da (Hani daga abin ƙi) sadaka ne, kai a cikin jima'in ɗayanku ma ga matarsa sadaka ne. Sai suka yi mamaki, suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama a cikinta akwai lada?! Ya ce; Shin kuna ganin da ace ya sanyata a cikin haram na zina ko waninsa shin zai zama akansa akwai zunubi? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada.
Fa'idoji
- Rige-rigen sahabbai akan aikata alheri, da kwaɗayinsu a cikin samun babban lada da falala daga wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Yawan kofofin ayyukan alheri, kuma su suna ƙunsar dukkan aikin da musulmi ya tashi da shi da niyya ta gari da kuma kyakkyawar manufa.
- Sauƙin Musulunci da rangwaminsa, kowane musulmi yana da abinda zai aikata shi dan ya bi Allah da shi.
- Nawawi ya ce: A cikin wannan akwai dalili akan cewa abubuwan da aka halatta suna zama ayyukan biyayya da niyyoyi na gaskiya, jima'i yana zama ibada idan ya yi nufin biyan haƙƙin mata da shi, da kuma mu'amalantarta da aikin alheri wanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi umarni da shi, ko neman ɗa na gari, ko kare kansa ko kare matar da hanasu gaba ɗaya daga kallon haram, ko tinani a cikinsa, ko nufinsa, ko wanin haka daga manufofi na gari.
- Buga misalai da ƙiyasi; dan ya zama ya fi bayyana kuma ya fi zama a cikin ran mai sauraro .
Sharhi: العربية
اشْتَكَى بعضُ فقراء الصحابة حالَهم وفقرَهم للنبيِّ صلى الله عليه وسلم وعَدَم تَصَدُّقِهم بالأموال لِيَحصلوا على الأجور الكثيرة كما حصل عليها إخوانُهم أصحاب المال الكثير وليفعلوا الخير مثلهم؛ حيث إنهم يُصلُّون كما نصلِّي، ويصومون كما نصوم، ويتصدقون بفضول أموالهم ولا نتصدق! فَدَلَّهم النبيُ صلى الله عليه وسلم على ما يقدرون عليه من الصدقات، فقال صلى الله عليه وسلم: أَوَلَيس قد جعل الله لكم ما تَصدّقون به على أنفسكم؟! فإنّ قولَكم: (سبحان الله) يكون لكم أجر صدقة، وكذا قول: (الله أكبر) صدقة، وقول: (الحمد لله) صدقة، وقول: (لا إله إلا الله) صدقة، و(الأمر بالمعروف) صدقة، و(النهي عن المنكر) صدقة، بل وفي جماع أحدكم لزوجته صدقة. فتعجَّبوا، وقالوا: يا رسول الله، أيأتي أحدُنا شهوتَه ويكونُ له فيها أجر؟! قال: أرأيتم لو وَضعها في حرامٍ مِن زنى أو غيره أكان عليه فيها إثم؟ فكذلك إذا وضعها في الحلال كان له أجر.
- تنافُس الصحابة على فعل الخيرات، وحرصهم في نيل عظيم الأجر والفضل من عند الله تعالى.
- كثرة وجوه أعمال الخير، وأنها تشمل كلَّ عمل يقوم به المسلم بنية صالحة وقَصْد حَسَن.
- يسر الإسلام وسهولته، فكل مسلم يجد ما يَعمله ليطيع الله به.
- قال النووي: وفي هذا دليل على أنَّ المباحات تصير طاعات بالنيات الصادقات، فالجماع يكون عبادة إذا نَوَى به قضاء حقّ الزوجة ومعاشرتها بالمعروف الذي أمر الله تعالى به، أو طلب ولد صالح، أو إعفاف نفسه أو إعفاف الزوجة ومنعهما جميعًا من النظر إلى حرام، أو الفكر فيه، أو الهم به، أو غير ذلك من المقاصد الصالحة.
- ضرب المثل والقياس؛ ليكون أوضح وأوقع في نفس السامع.