Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «أَحَبُّ الْبِلَادِ إِلَى اللهِ مَسَاجِدُهَا، وَأَبْغَضُ الْبِلَادِ إِلَى اللهِ أَسْوَاقُهَا».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi soyuwar gurare a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka - sune masallatan garuruwan; domin su wuraran ayyukan biyayya ga Allah ne, kuma ginshiƙansu akan tsoron Allah ne. Kuma mafi ƙin garuruwa a wajen Allah sune kasuwanninsu; domin cewa galibi guri ne na algus da yaudara da riba da rantse-rantse akan ƙarya, da saɓa alƙawari, da bijirewa ambatan Allah.
Fa'idoji
- Alfarmar masallatai da gurarensu; domin su gidajen da ake ambatan Allah da yawa ne a cikinsu.
- Kwaɗaitarwa akan lazimtar masallatai, da yawan kaikawo zuwa garesu, dan neman soyayyar Allah - Maɗaukakin sarki - da yardarSa, da kuma ƙaranta kaikawo zuwa ga kasuwanni, sai dan buƙata; dan nisanta daga faɗawa cikin sabubban ƙiyayyar (Allah).
- Imam Nawawi ya ce: Masallatai gurare ne na saukar rahama, kasuwanni kuwa kishiyarsu ne.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن أحب الأماكن إلى الله عز وجل مساجدها؛ لأنها بيوت الطاعات، وأساسها على التقوى، وأبغض البلاد إلى الله أسواقها؛ لأنها غالبًا محل الغش والخداع والربا والأيمان الكاذبة وإخلاف الوعد والإعراض عن ذكر الله.
- حرمة المساجد ومكانتها؛ لأنها بيوت يذكر فيها اسم الله كثيرًا.
- الحث على لزوم المساجد، وكثرة التردد إليها، طلبًا لمحبة الله تعالى ومرضاته، وعلى تقليل التردد إلى الأسواق، إلا للحاجة؛ تجنبًا عن الوقوع في أسباب المَقْت.
- قال النووي: المساجد محل نزول الرحمة والأسواق ضدها.