Hadisai

Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «أَتَدْرُونَ مَا الْغِيبَةُ؟»، قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «ذِكْرُكَ أَخَاكَ بِمَا يَكْرَهُ»، قِيلَ: أَفَرَأَيْتَ إِنْ كَانَ فِي أَخِي مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «إِنْ كَانَ فِيهِ مَا تَقُولُ فَقَدِ اغْتَبْتَهُ، وَإِنْ لَمْ يَكُنْ فِيهِ فَقَدْ بَهَتَّهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka ambaci ɗan uwanka da abin da yake ƙi", aka ce: Shin kana ganin in ya kasance akwai abin da nake faɗa a kan ɗan uwana fa? sai ya ce: "Idan ya kasance a cikinsa akwai abin da kake faɗa, to, haƙiƙa ka yi gibarsa, idan babu (abin da kake faɗa) a cikinsa, to, haƙiƙa ka ƙirƙirar masa ƙarya".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haƙiƙanin gibar da aka haramta, ita ce: Ambaton musulmi mai gibar da abin da yake ki, daidai ne ya kasance daga siffofinsa ne na halitta ko na ɗabi'a, kamar: Mai ido ɗaya mai yawan algus maƙaryaci, da makamancin hakan daga siffofin zargi, ko da waɗannan siffofin sun kasance samammu ne a gareshi. Amma idan babu siffar a tare da shi, to, wannan ya fi tsanani daga giba, shi ne ƙirƙirar ƙarya, wato: Ƙirkirar abin da babu a tare da shi.

Fa'idoji

  • Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ta inda yake jefa mas'aloli ta hanyar tambaya.
  • Kyakkyawan ladabin sahabbai tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yayin da suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani.
  • Faɗin wanda aka tamabaya abin da bai sanshi ba; Allah ne mafi sani.
  • Karewar shari'a ga zamatakewa ta hanyar kare haƙƙoƙi da 'yan uwantaka a tsakaninsu.
  • Giba abar haramtawa ce sai a wasu halaye dan maslaha; daga hakan akwai: Tunkuɗe zalunci, ta yadda wanda aka zalunta zai ambaci wanda ya zalunceshi ga wanda zai iya karɓa masa haƙƙinsa, sai ya ce: Wane ya zalunceni, ko ya yi min kaza, daga ciki akwai: Shawara a al'amarin aure ko tarayya ko maƙotaka, da makancin hakan.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم حقيقة الغيبة المُحرَّمة، وهي: ذِكْرُ المسلم الغائب بما يَكره، سواء كان من صفاته الخَلْقية أو الخُلُقية، مثل: الأعور الغشاش الكذاب، ونحو ذلك من صفات الذم، ولو كانت تلك الصفة موجودة فيه. وأما إذا لم تكنْ فيه الصفةُ فهذا أشدُّ من الغيبة، وهو البُهْتَان، أي: الافتراء على الإنسان بما ليس فيه.

  • حُسْن تعليم النبي صلى الله عليه وسلم، حيث يُلقي المسائل على طريقة السؤال.
  • حُسْن أدب الصحابة مع النبي صلى الله عليه وسلم، حين قالوا: الله ورسوله أعلم.
  • قول المسؤول عن ما لا يعلمه: الله أعلم.
  • صيانة الشريعة للمجتمع بحفظ الحقوق والأخوة بينهم.
  • الغيبة محرمة إلا في بعض الأحوال للمصلحة؛ ومن ذلك: دفع الظلم، بحيث يَذكرُ المظلومُ مَن ظَلَمَه عند من يستطيع الأخذ بحقه، فيقول: ظلمني فلان، أو فعل بي كذا، ومنها: المشاورة في أمر الزواج أو المشاركة أو المجاورة، ونحو ذلك.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari