Hadisai

Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwala sannan ya zo Juma'a sai ya saurari huduba kuma ya yi shiru za'a gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin Juma'a da ƙarin kwanaki uku

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ ثُمَّ أَتَى الْجُمُعَةَ فَاسْتَمَعَ وَأَنْصَتَ غُفِرَ لَهُ مَا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجُمُعَةِ وَزِيَادَةُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ، وَمَنْ مَسَّ الْحَصَى فَقَدْ لَغَا».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwala sannan ya zo Juma'a sai ya saurari huduba kuma ya yi shiru za'a gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin Juma'a da ƙarin kwanaki uku, wanda ya taba tsakankwani to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalarsa da cikawa da zuwa da sunnoninta da ladubbanta, sannan ya zo sallar Juma'a kuma ya yi shiru ya karkata ga mai huɗuba, kuma ya yi shiru daga yashasshiyar magana; za'a gafarta masa ƙananan zunuban kwana goma, daga sallar Juma'a zuwa Juma'a ta biyu da ƙarin kwanuka uku; domin kyakkyawa da kwatankwacinta goma. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga rashin fuskantar zuciya ga abinda ake faɗa a cikin huɗuba na wa'azuzzuka, da kuma wasa da gabbai na shafar tsakwankwani da waninsu na nau’ukan wasa da shagaltuwa, cewa wanda ya aikata hakan to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana, wanda ya yi yashasshiyar magana to ba shi da rabo a cikin ladan Juma'a cikakkiya.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan yin alwala da cikata da kammalata, da kiyayewa akan sallar Juma'a.
  • Falalar sallar Juma'a.
  • Wajabcin yin shiru a huɗubar Juma'a, da rashin shagaltuwa daga gareta da zance da waninsa.
  • Wanda ya yi yashasshiyar magana a lokacin huɗuba to sallar Juma'ar ta yi kuma ta dauke farilla, tare da rage lada.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن توضأ فأحسن وضوءه بإتمام أركانه والإتيان بسننه وآدابه، ثم أتى صلاة الجمعة وأنصت وأصغى للخطيب، وسكت عن اللغو؛ غفر الله له صغائر ذنوب عشرة أيام، من صلاة الجمعة إلى الجمعة الثانية وزياة ثلاثة أيام؛ لأن الحسنة بعَشر أمثالها، ثم حذَّر صلى الله عليه وسلم من عدم إقبال القلب عمّا يقال في الخطبة من مواعظ، ومِن عَبَثِ الجوارح مِن مَسِّ الحصى وغيره من أنواع العبث والانشغال، بأنَّ مَن فَعل ذلك فقد لغا، ومن لغا فلا حظ له في أجر جمعة كاملة.

  • الحث على أداء الوضوء وإتمامه على كمال، والمحافظة على صلاة الجمعة.
  • فضل صلاة الجمعة.
  • وجوب الإنصات لخطبة الجمعة، وعدم التشاغل عنها بالكلام وغيره.
  • من لغا أثناء الخطبة فصلاة الجمعة مجزئة ومسقطة للفرض، مع نقص الأجر.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari