Hadisai

Ni'imomi biyu ana yi wa da yawa daga mutane kamunga a cikinsu: Lafiya da rarar lokaci

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «نِعْمَتَانِ مَغْبُونٌ فِيهِمَا كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ: الصِّحَّةُ وَالفَرَاغُ».

Fassara

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ni'imomi biyu ana yi wa da yawa daga mutane kamunga a cikinsu: Lafiya da rarar lokaci".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ni'imomi biyu masu girma daga ni'imomin Allah ga mutum wanda da yawa daga mutane suke hasara a cikinsu inda suke juyar da su ba'a mahallinsu ba; domin mutum idan ni'imar lafiya tare da rarar lokaci suka taru gare shi , sai kasala ta rinjaye shi daga ɗa'a to shi yana daga masu hasara; wannan shi ne halin mafi yawancin mutane, idan ya yi anfani da rarar lokaci da kuma lafiyarsa a cikin ɗa'ar Allah to shi mai rabauta ne; inda kuma duniya ita ce gonar lahira, kuma a cikinta akwai kasuwancin da ribarsa take bayyana a lahira, rarar lokaci kuma shagalta tana biye masa, lafiya kuwa rashin lafiya yana biye mata, koda baikasance ba sai tsufa da to ya isa

Fa'idoji

  • Kamanta mukallafi da ɗan kasuwa, lafiya kuma da rarar lokaci da jari; wanda ya kyautata amfani da jarinsa to zai samu kuma za ci riba, wanda ya tozartar da shi zai yi hasara da nadama.
  • Ibnu Khazin ya ce: Ni'ima ita ce abinda mutum yake ni'imtuwa da ita kuma yake jin daɗinta, kamunga kuwa ita ce mutum ya sayi (abu) da ninkin kuɗinsa, ko ya siyar da ƙasa da farashi irin nasa; wanda jikinsa ya samu lafiya kuma ya shagaltu da ƙoƙari bai sami sarari dan gyara lahirarsa ba to shi kamar wanda aka yi wa kamunga ne a cikin ciniki.
  • Kwaɗayi akan amfanuwa lafiya da kuma rarar lokaci dan neman kusanci ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da kuma aikata alherai kafin kufcewarsu.
  • Godewa ni'imomin Allah yana kasancewa ne da yin amfani da su a cikin biyayya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Alƙali Abubakar ɗan Arabi ya ce: An yi saɓani a cikin farkon ni'imar Allah akan bawa, aka ce: Imani, kuma an ce: Rayuwa, an ce kuma: Lafiya, na farkon ya fi domin cewa shi ni'ima ce kai tsaye, amma rayuwa da lafiya to cewa su ni'ima ce ta duniya, kuma basa kasancewa ni'ima ta haƙiƙa sai idan ta kasance da imani, to a wannan lokacin za’a yi wa mutane da yawa kamunga a cikinsu, wato ribarsu zata tafi ko ta ragu, wanda ya sakarwa ransa mai umarni da mummuna mai dawwamarwa zuwa hutu sai ya bar kiyayewa akan iyakokin (Allah), da lazimta akan ɗa'a to haƙiƙa an yi masa kamunga, haka nan idan ya zama mai rarar lokaci, domin cewa wanda aka shagaltar zai iya kasancewa yana da uzuri sabanin mai rarar lokaci; cewa shi uzuri zai dauke daga gare shi kuma hujja ta tsayu a kansa.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن نعمتين عظيمتين من نعم الله على الإنسان يَخْسَر فيهما كثيرٌ من الناس حيث يَصرفونها في غير محلها؛ فإن الإنسان إذا اجتمع له نعمة الصحة مع الفراغ، فغَلَبَ عليه الكسل عن الطاعة فهو الخاسر؛ وهي حال أكثر الناس، وإن استعمل فراغَه وصحتَه في طاعة الله فهو الرابح؛ حيث أن الدنيا مزرعة الآخرة، وفيها التجارة التي يظهر ربحُها في الآخرة، والفراغ يَعْقُبُه الشُّغْل، والصحة يعقبها السَّقَم، ولو لم يكن إلا الهَرَم لَكَفى.

  • تشبيه المكلَّف بالتاجر، والصحة والفراغ برأس المال؛ فمن أحسن استخدام رأس ماله نال وربح، ومن ضيَّعه خَسِر ونَدِم.
  • قال ابن الخازن: النعمة ما يتنعّم به الإنسان ويَستَلِذُّه، والغَبْنُ أنْ يشتري بأضعاف الثمن، أو يبيع بدون ثمن المِثْل؛ فمن صحَّ بدنه وتَفَرّغ من الأشغال العاتقة ولم يَسْعَ لصلاح آخرته فهو كالمغبون في البيع.
  • الحرص على الاستفادة من الصحة والفراغ للتقرب إلى الله عز وجل، وفعل الخيرات قبل فواتهما.
  • شكر نعم الله يكون باستخدامها في طاعة الله تعالى.
  • قال القاضي وأبو بكر بن العربي: اختلف في أول نعمة الله على العبد، فقيل: الإيمان، وقيل: الحياة، وقيل: الصحة، والأول أولى فإنه نعمة مُطْلَقة، وأما الحياة والصحة فإنهما نعمة دنيوية، ولا تكون نعمة حقيقة إلا إذا صاحبت الإيمانَ، وحينئذ يُغْبَنُ فيها كثير من الناس، أي يذهب رِبْحُهم أو يَنْقُص، فمَن استرسل مع نفسه الأمّارة بالسوء الخالدة إلى الراحة فترك المحافظة على الحدود، والمواظبة على الطاعة فقد غُبِنَ، وكذلك إذا كان فارغًا، فإنّ المشغول قد يكون له مَعذِرة بخلاف الفارغ؛ فإنه يرتفع عنه المعذرة وتقوم عليه الحجة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari