Hadisai

‌Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عِيَاضِ بْنِ حِمَارٍ أَخِي بَنِي مُجَاشِعٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَامَ فِينَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ خَطِيبًا، فَقَالَ: وَسَاقَ الْحَدِيثَ وَفِيهِ: «وَإِنَّ اللهَ أَوْحَى إِلَيَّ أَنْ تَوَاضَعُوا حَتَّى لَا يَفْخَرَ أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ، وَلَا يَبْغِي أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ».

Fassara

Daga Iyad ɗan Himar ɗan uwan Mujashi'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu yana mai yin huɗuba, sai ya ce: Sai ya koro hadisin kuma a cikinsa: «‌Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a cikin sahabbansa yana mai huɗuba, ya kasance daga cikin abinda ya ce: Lallai cewa Allah Ya yi masa wahayi cewa ya wajaba akan mutane su yi tawali'u a tsakaninsu, hakan ta hanyar ƙanƙar da kai ga halitta da tausasa lamura, har kada wani ya yi alfahari ta hanyar da'awar girma da kafafa da ɗaukakar da zai danganta kansa ko dukiyarsa ko wanin haka akan wani, kuma kada wani ya zalinci wani, kuma kada ya yi ta'addaci akan wani.

Fa'idoji

  • A cikin hadisin akwai kwaɗaitarwa akan tawali'u da rashin girman kai da rena mutane.
  • Hani daga zalinci da kuma alfahari.
  • Yi wa Allah tawali'u yana da ma'anoni biyu: Ma'ana ta farko: Ita ce, ka yi wa Addinin Allah tawali'u, kada ka rena Addini, kuma kada ka yi masa girman kai akan sauke hukunce-hukuncensa. Na biyu: Ka yi wa bayin Allah tawali'u saboda Allah, badan tsoronsu ba, ba kuma dan kwaɗayin abinda ke gurinsu ba, sai dai saboda Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Sharhi: العربية

قام النبي صلى الله عليه وسلم في أصحابه خطيبًا، وكان مما قال: إن الله أوحى إليه أنه يجب على الناس أن يتواضعوا فيما بينهم، وذلك بخفض الجناح للخلق ولين الجانب، حتى لا يفخر بادعاء العظمة والكبرياء والشرف أحدٌ بنسبه أو ماله أو غير ذلك على أحد، ولا يظلم ولا يعتدي أحدٌ على أحد.

  • في الحديث الحث على التواضع وعدم الكبر والترفع على الناس.
  • النهي عن البغي والفخر.
  • التواضع لله له معنيان: المعنى الأول: أن تتواضع لدِينِ الله، فلا تترفع عن الدِّين، ولا تستكبر عنه وعن أداء أحكامه، والثاني: أن تتواضع لعباد الله من أجل الله، لا خوفًا منهم، ولا رجاءً لما عندهم، ولكن لله عزَّ وجلَّ.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari