Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنهما أنَّ رَسولَ اللَّهِ صلَّى اللَّهُ عليْه وسلَّمَ، قال: «قَدْ أَفْلَحَ مَن أَسْلَمَ، وَرُزِقَ كَفَافًا، وَقَنَّعَهُ اللَّهُ بما آتَاهُ».
Fassara
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa haƙiƙa ya rabauta wanda ya miƙa wuya ga Ubangijinsa sai aka shiryar da shi kuma aka datar da shi ga Musulunci, kuma aka azirta shi gwagwadan buƙatarsa daga halal ba tare da ƙari ko ragi ba, kuma Allah Ya sanya shi mai yarda da abinda Ya bashi.
Fa'idoji
- Kwanciyar hankalin mutum yana cikin cikar Addininsa da isuwar abin cinsa da kuma wadatuwarsa da abinda Allah Ya ba shi.
- Kwaɗaitarwa a kan wadatuwa da abinda aka baka na duniya tare da Musulunci da kuma sunnah.
Sharhi: العربية
بيّن النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه قد فاز وظفر مَن انقاد إلى ربه فَهُدِي ووفق للإسلام، ورزق من الحلال قدْر حاجته من غير زيادة ولا نقص، وجعله الله قانعًا راضيًا بما أعطاه.
- سعادة المرء في كمال دينه وكفاف عيشه وقناعته بما آتاه الله.
- الترغيب في القناعة بما أوتيت من الدنيا مع الإسلام والسنة.