Hadisai

Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «الْحَلِفُ مَنْفَقَةٌ لِلسِّلْعَةِ، مَمْحَقَةٌ لِلرِّبْحِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi akan rantsuwa da kuma yawaita ta koda ta kasance akan gaskiya ne a siye da siyarwarsa, kuma ya bada labarin cewa ita sababi ce ta yawaitar haja da kaya da kuma samun ribarsu, sai dai hakan tawaya ce kuma ɓata albarkar riba ce da kuma kasuwanci, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai iya dora wasu abubuwa da zasu ɓata su kodai ta hanyar sata ko gobara ko dilmiya a ruwa ko ƙwace ko fizge ko wasu abubuwa masu bijirowa daban waɗanda dukiyarsa zata lalace saboda su.

Fa'idoji

  • Girmama al'amarin rantsuwa da Allah, kuma cewa ita ba ta kasancewa sai dan wata buƙata.
  • Kasuwanci na haram koda girmansa ya yawaita; to shi abin cirewa albarka ne babu alheri a cikinsa.
  • AlƘari ya ce: Tafiyar albarkar abin kasuwanci; kodai dan lalacewa ne wanda zai riske shi a cikin dukiyarsa, ko dan ciyar da shi a abinda anfaninsa ba zai koma zuwa gare shi ba a nan duniya ko ladansa a nan gaba (lahira), ko ya wanzu a wurinsa kuma a haramta masa anfaninsa, ko wanda ba zai gode masa ba ya gaje Shi.
  • Annawawi ya ce: A cikinsa akwai hani akan yawan rantsuwa a cikin ciniki, domin rantsuwa ba tare da wata buƙata ba abin ƙi ce, kuma zai haɗa da yawaitar haja gare shi, wataƙila mai siye ya ruɗu da rantsuwar.
  • Yawan rantsuwa tawaya ne a imani, kuma tawaya ne a cikin Tauhidi; domin cewa yawan rantsuwa yana kaiwa zuwa abubuwa biyu: Na farkonsu: Sakaci a cikin hakan da rashin kulawa, al'amari na biyu: Ƙarya, domin cewa duk wanda rantsuwarsa ta yawaita zai afka cikin ƙarya, to ƙaranta hakan yana kamata da kuma rashin yawaita rantsuwa, saboda haka ne tsarki ya tabbatar maSa Ya ce: {Ku kiyaye rantse-rantsenku} [al-Ma'idah: 89].
Sharhi: العربية

حَذَّرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم مِن الحَلِف والإكثار منه حتى لو كان صادقًا في البيع والشراء، وأخبر أنه سبب لِرَوَاج السلعة والمتاع، لكنه نَقْصٌ وإبطال لبركة الربح والكسب، وقد يُسلِّط الله تعالى عليه وُجوهًا يَتْلَف فيها إما سَرْقًا أو حَرْقًا أو غَرَقًا أو غصبًا أو نهبًا أو عوارض أخرى يتلف بها ماله.

  • تعظيم أمر الحلف بالله، وأنه لا يكون إلا لحاجة.
  • الكسب الحرام وإن كَثُرَت كَمِّيّته؛ فإنه مَنزوع البركة لا خير فيه.
  • قال القاري: ذهاب بركة المكسوب؛ إما بتلف يلحقه في ماله، أو بإنفاقه في غير ما يعود نفعه إليه في العاجل أو ثوابه في الآجل، أو بقي عنده وحُرِم نفعه، أو وَرِثَه مَن لا يَحْمَدُه.
  • قال النووي: فيه النهي عن كثرة الحلف في البيع، فإن الحلف من غير حاجة مكروه، وينضم إليه ترويج السلعة، وربما اغترَّ المشتري باليمين.
  • كثرة الحلف نقص في الإيمان، ونقص في التوحيد؛ لأن كثرة الحلف تفضي إلى شيئين: أحدهما: التساهل في ذلك وعدم المبالاة، والأمر الثاني: الكذب، فإن من كثرت أيمانه وقع في الكذب، فينبغي التَّقَلُّلُ من ذلك وعدم الإكثار من الأيمان، ولهذا قال سبحانه: (وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ) [المائدة:89].

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari