Hadisai

Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه: أَنَّ نَفَرًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَأَلُوا أَزْوَاجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ عَمَلِهِ فِي السِّرِّ؟ فَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا أَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، وَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا آكُلُ اللَّحْمَ، وَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا أَنَامُ عَلَى فِرَاشٍ، فَحَمِدَ اللهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ، فَقَالَ: «مَا بَالُ أَقْوَامٍ قَالُوا كَذَا وَكَذَا؟ لَكِنِّي أُصَلِّي وَأَنَامُ، وَأَصُومُ وَأُفْطِرُ، وَأَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، فَمَنْ رَغِبَ عَنْ سُنَّتِي فَلَيْسَ مِنِّي».

Fassara

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun tambayi matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikinsa a ɓoye? sai sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba, sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba, sashinsu ya ce: Ba zan yi bacci akan shinfiɗa ba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sai ya ce: "Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni".

Sharhi

Wasu mutane cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun zo ɗakunan matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suna tambaya game da ibadarsa a ɓoye a cikin gidansa, lokacin da aka ba su labari kamar cewa su sunga ƙanƙantarta, sai suka ce: Wane mu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ? haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa da abinda ya jinkirta, saɓanin wanda bai san faruwar gafara gare shi ba to yana buƙatuwa zuwa kai matuƙa a cikin ibada wataƙila ya sameta. Sannan sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan yi bacci a kan shinfiɗa ba. Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi fushi, ya yi wa mutane huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi ya ce: Menene sha'anin wasu mutane ne sun ce kaza da kaza?! Na rantse da Allah lallai cewa nine mafi tsoronku ga Allah kuma mafi taƙawarku gare shi, sai dai cewa ni ina bacci dan in samu ƙarfi akan tsayuwar (dare), kuma ina buɗe baki dan in samu ƙarfin azimi, kuma ina auren mata, wanda ya bijire daga hanyata kuma ya ga cika a waninta, ya riƙi hanyar wanina to ba ya tare da ni.

Fa'idoji

  • Son sahabbai - Allah Ya yarda da su - ga alheri, da kuma kwaɗayinsu a cikinsa da kuma koyi da Annabinsu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Sauƙin wannan shari'ar da rangwaminta, dan riƙo daga aikin Annabinta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma shiriyarsa.
  • Alheri da albarka (suna) cikin koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da bin halayensa maɗaukaka.
  • Tsawatarwa daga tsanantawa kai a cikin ibadu da abinda ba zaka iya ba, kuma wannan yana daga halin 'yan bidi'a.
  • Ibnu Hajar ya ce: Riƙo da tsanantawa a cikin ibada yana kaiwa zuwa ƙosawa mai yanke asalin ibadar, kuma lazimtar taƙaituwa akan farillai misali, da barin nafilfili yana kaiwa zuwa fifita hutun sangarcewa, da rashin nishaɗi zuwa ga ibada, kuma mafificin al'amura tsaka-tsaki.
  • a cikinsa akwai bibiyar halayen manya dan yin koyi da ayyukansu, kuma cewa shi idan saninsa daga maza ya yi wahala to neman yayewarsa daga mata ya halatta.
  • A cikinsa akwai wa'azi da jefa mas'alolin ilimi da bayanin hukunce-hukunce ga mukallafai, da kawar da shubuha daga masu ijtihadi.
  • Umarni da sauƙaƙawa a cikin ibada, tare da kiyayewa a kanta da kuma farillai da nafilfili; dan musulmi ya kiyaye haƙƙoƙin waninsa a kansa.
  • a cikin hadisin akwai nuni akan falalar aure da kwaɗaitarwa a cikinsa.
Sharhi: العربية

جَاءَ نَفَرٌ من الصحابة رضي الله عنهم إلى بيوت أزواج النبي صلى الله عليه وسلم، يسألون عن عبادته في السر داخل بيته، فلما أُخبروا كأنهم تَقَالُّوها، فقالوا: وأين نحن من النبي صلى الله عليه وسلم؟ قد غُفر له ما تقدم من ذنبه وما تأخر، بخلاف مَن لم يعلم بحصول المغفرة له فيحتاج إلى المبالغة في العبادة عسى أن يَحصُل عليها. ثم قال بعضهم: لا أتزوج النساء. وقال بعضهم: لا آكل اللحم. وقال بعضهم: لا أنام على فراش. فبلغ ذلك النبيَّ صلى الله عليه وسلم، فغضب، وخطب الناس، فحمد الله وأثنى عليه وقال: ما شَأْنُ أقوامٍ قالوا كذا وكذا؟! والله إني لأخشاكم لله وأتقاكم له، لكني أنام لأتقوى على القيام، وأفطر لأتقوَّى على الصوم، وأتزوج النساء، فمن أعرض عن طريقتي ورأى الكمال في غيرها، وأخذ بطريقة غيري فليس مني.

  • حب الصحابة رضي الله عنهم للخير، ورغبتهم فيه وفى الاقتداء بنبيهم صلى الله عليه وسلم.
  • سماحة هذه الشريعة ويسرها، أخذًا من عمل نبيها صلى الله عليه وسلم وهديه.
  • الخير والبركة في الاقتداء بالنبي صلى الله عليه وسلم، واتباع أحواله الشريفة.
  • الزَّجْر عن التشديد على النفس في العبادات بما لا تطيق، وأن هذا من حال المبتدعين.
  • قال ابن حجر: الأخذ بالتشديد في العبادة يُفضي إلى المَلَل القاطِع لأصلها، وملازمة الاقتصار على الفرائض مثلًا، وترك التنفُّل يفضي إلى إيثار البطالة، وعدم النشاط إلى العبادة، وخير الأمور الوسط.
  • فيه تتبُّع أحوال الأكابر للتأسِّي بأفعالهم، وأنه إذا تعذَّرت معرفته من الرجال جاز استكشافه من النساء.
  • فيه الوعظ وإلقاء مسائل العلم وبيان الأحكام للمكلَّفين، وإزالة الشبهة عن المجتهدين.
  • الأمر بالترفُّق في العبادة، مع المحافظة عليها وعلى الفرائض والنوافل؛ ليراعي المسلم حقوق غيره عليه.
  • في الحديث دلالة على فضل النكاح والترغيب فيه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari