Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ يَزِيدَ الخَطْمِيِّ قَالَ: حَدَّثَنِي البَرَاءُ وَهُوَ غَيْرُ كَذُوبٍ، قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا قَالَ: سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، لَمْ يَحْنِ أَحَدٌ مِنَّا ظَهْرَهُ حَتَّى يَقَعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَاجِدًا، ثُمَّ نَقَعُ سُجُودًا بَعْدَهُ.
Fassara
Daga Abdullahi bn Yazid al-Khaɗmi ya ce: Bara'u ya zantar da ni alhali shi ba maƙaryaci ba ne, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ce: Sami'allahu liman hamidahu (Allah Yaji wanda ya gode maSa) wani ɗaya daga cikinmu baya sunkuyar da bayansa har sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi yana mai sujjada, sai muma mu faɗi muna masu sujjada a bayansa.
Sharhi
Bara'au Dan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari alhali shi mai gaskiyane, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Sami'al lahu liman hamidahu (Allah Yaji wanda ya gode maSa), wanda ke bayansa ba ya gushewa a tsaye, kuma wani ba ya sunkuyar da bayansa dan yin sujjada har sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanya goshinsa akan ƙasa, sannan su faɗi suna masu sujjada a bayansa.
Fa'idoji
- Siffar biyayyar sahabbai ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin sallah, kuma cewa su basa sunkuyawa daga tsayuwa zuwa sujjada har sai ya yi sujjada.
- Ibnu Daƙiƙul id ya ce: A cikin haka akwai dalili akan tsawon nutsuwa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Akwai halaye huɗu ta ɓangaren koyin mamu tare da limaminsa: 1- Rigaya: Shi ne ya fara yin abu kafin limamainsa, shi ne mamu ya kai ga rukuni kafin liman ya kai ga wannan rukunin, misali: Ya yi ruku'u kafin liman ya yi ruku'u, ko ya yi sujjada kafin liman ya yi sujjada, to wannan haramun ne, idan ya riga da gangan tare da cewa ya san hakan haramun ne to lallai sallarsa ta ɓaci, daidai ne ya riga shi yin rukuni ne ko kuma ya rigayeshi zuwa rukuni, idan a kabbarar harama ne to sallar sa ma bata ƙullu ba, kuma ya wajaba agare shi ya sake sallah daga farko. 2- Daidaitawa: Shi ne ya zama ya yi daidai da liman, ya yi ruku'u tare da ruku'unsa kuma ya yi sujjada tare da sujjadarsa kuma ya taso tare da tasowarsa, wannan mafi ƙarancin halayensa ya zama makruhi, amma zahirin dalilai cewa hakan haramun ne, idan ya yi daidai da liman a kabbarar harama to sallarsa bata yi ba kuma waibi ne ya saketa. 3- Bi: Shi ne ya zo da ayyukan sallah bayan limaminsa ba tare da wani jinkiri ba, wannan shi ne abin da aka shara'anta kuma ya dace da sunnah. 4- Saɓawa: Shi ne ya saɓawa limaminsa saɓawar da zata iya fitar da shi daga bi, kamar liman ya yi riku'u amma mamu ya tsaya a tsaye har liman ya kusa ɗagowa daga ruku'u, to wannan saɓanin abin da aka shara'anta ne, kuma hakan haramun ne, sai inda wani uzuri, kamar rashin lafiya da kuma tsufa.
Sharhi: العربية
يخبر البراء ابن عازب رضي الله عنه وهو صادق، أن النبي صلى الله عليه وسلم كان إذا رفع رأسه من الركوع وقال: سمع الله لمن حمده، لم يزل من خلفه قيامًا، ولم يثنِ أحدٌ ظهره للسجود حتى يضع صلى الله عليه وسلم جبهته على الأرض، ثم يقعون سجودًا بعده.
- صفة متابعة الصحابة للرسول صلى الله عليه وسلم في الصلاة، وأنهم لا ينتقلون من القيام إلى السجود حتى يسجد.
- قال ابن دقيق العيد: في ذلك دليل على طول الطمأنينة من النبي صلى الله عليه وسلم.
- للمأموم مع إمامه أربع حالات من حيث الاقتداء: 1- مسابقة: بأن يبدأ بالشيء قبل إمامه، بأن يصل المأموم إلى الرُّكن قبل أن يصل إليه الإمام، مثل: أن يركع قبل ركوع الإمام، أو يسجد قبل سجود الإمام، وهذا حرام، وإذا تعمَّد السبق مع عِلْمه بالنهي فإنَّ صلاته تبطل، سواء سبقه بركن أو سبقه إلى الركن، وإذا كان في تكبيرة الإحرام لم تنعقد صلاته، ويجب عليه أن يعيدَ الصلاة من جديد. 2- موافقة: بأن يكون موافقًا للإمام، يركع مع ركوعه ويسجد مع سجود وينهض مع نهوضه، وهذا أقلُّ أحواله الكراهة، وظاهر الأدلة أنَّها محرَّمة أيضًا؛ وإذا وافقَ الإمامَ في تكبيرة الإحرام لم تنعقِد صلاتُه وعليه الإعادة. 3- متابعة: بأن يأتي بأفعال الصلاة بعد إمامه بدون تأخُّر، وهذا هو المشروع والموافق للسُّنَّة. 4- تخلُّف: بأن يتخلَّف عن إمامه تخلُّفًا يُخرِجه عن المتابعة، كأن يركع الإمام ويبقى المأموم قائمًا إلى أن يقرب الإمام من الرفع من الرُّكوع، وهذا خلاف المشروع، وهو حرام، إلا إن كان من عذر كمرض وكبر.