Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدَ النَّاسِ، وَكَانَ أَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي رَمَضَانَ حِينَ يَلْقَاهُ جِبْرِيلُ، وَكَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ مِنْ رَمَضَانَ فَيُدَارِسُهُ القُرْآنَ، فَلَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدُ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ.
Fassara
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi kyauta cikin mutane, kuma ya kasance mafi kyutar da yake yi a Ramadan ne lokacin da Jibril ya haɗu da shi, ya kasance yana haɗuwa da shi a cikin kowane dare na Ramadan sai su yi nazaran shi AlƘu'ani, to Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta ta alheri daga iskar da aka aiko.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi girman mutane a kyauta, ya kasance kyautarsa tana yawaita a cikin watan Ramadan lokacin da ya kasance yana bada abinda yake kamata ga wanda ya kamata, kuma sababi a cikin ƙaruwar kyautarsa abubuwane biyu: Na farko: Haɗuwarsa da Jibril - aminci ya tabbata agare shi -. Al'amari na ƙarshe: Karatun AlƘur'ani, shine karatu na zuciya. Sai nazarin da Jibril - aminci ya tabbata agare shi - yake yi da shi dukkan abinda ya sauka na AlƘur'ani ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne mafi kyauta mafi yawan bayarwa kuma mafi aikata alheri, kuma mafi gaggawar anfanar da halitta daga iska mai daɗi wacce Allah Yake aikota da girgije da kuma rahama.
Fa'idoji
- Bayanin kyautar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da yalwar kayutarsa musamman ma acikin watan Ramadan, cewa shi ne watan ayyukan biyayya da kuma lokutan alkhairai.
- Kwaɗaitarwa akan kyauta a cikin kowane lokaci, kuma an so ƙarawa a cikin watan Ramadan.
- Yawaita bayarwa da kyauta da kyautatawa da karatun AlƘur'ani a cikin watan Rmadan.
- Daga sabubban haddace ilimi akwai karatunsa tare da ɗaliban ilimi da kuma malamai.
Sharhi: العربية
كَانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أعظم الناس كَرمًا، وكان يَكثر كرمُه في شهر رمضان حيث كان يُعطي ما ينبغي لمَن ينبغي، والسبب في زيادة كرمه أمران: الأول: الْتِقاؤه بجبريل عليه السلام. والأمر الآخر: مدارسة القرآن، وهو القراءة عن ظهر قلب. فيدارسه جبريل عليه السلام جميع ما نزل من القرآن، ولَرَسُول الله صلى الله عليه وسلم أكرم وأكثر عطاءً وفعلًا للخير، وأسرع نفعًا للخلق من الريح الطيبة التي يرسلها الله بالغيث والرحمة.
- بيان جُود النبي صلى الله عليه وسلم وسَعَة كرمه وخاصة في رمضان، فإنه شهر الطاعات ومواسم الخيرات.
- الحث على الجود في كل وقت، وتستحب الزيادة في شهر رمضان.
- الإكثار من البذل والعطاء والإحسان وقراءة القرآن في شهر رمضان.
- من أسباب حفظ العلم مدارسته مع طلاب العلم والعلماء.