Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ أبي زُهير عُمَارَةَ بْنِ رُؤَيْبَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: «لَنْ يَلِجَ النَّارَ أَحَدٌ صَلَّى قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا»
Fassara
Daga Abu Zauhair ɗan Ru'aibatu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba".
Sharhi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Babu wani ɗaya wanda ya sallaci sallar Asuba, da sallar La'asar kuma ya dawwama a kansu da zai shiga wuta; ya keɓanci waɗannan salloli biyun; domin cewa su ne mafi nauyin salloli, kuma cewa lokacin safiya yana kasancewa ne lokacin bacci da daɗinsa, lokacin La'asar kuma yana kasancewa ne a lokacin shagaltuwa da ayyukan yini da kuma kasuwancinsa, wanda ya kiyaye akan waɗannan salloli biyun tare da samun wahala to zai kiyaye akan ragowar sallolin.
Fa'idoji
- Falalar salloli biyu Asuba da La'asar, to kiyayewa akansu yana wajaba.
- Wanda ya yi waɗannan sallolin zai zama galibi ba shi da kasalar zuciya da kuma riya, kuma mai son ibada.
Sharhi: العربية
يُخْبِرُ رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: أنه لن يدخلَ النارَ، أحدٌ صلّى صلاة الفجر، وصلاة العصر، وداوم عليهما؛ وخَصَّ هاتين الصلاتين؛ لأنهما أثقلُ الصلوات، ولأنّ وقت الصبح يكون عند النوم ولَذَّتِه، ووقت العصر يكون عند الاشتغال بأعمال النهار وتجارته، ومَن حافَظَ على هاتين الصلاتَين مع وُجودِ المَشقّة فسيحافظ على بَقيّة الصلوات.
- فضل صلاتي الصبح والعصر، فينبغي المحافظة عليهما.
- مَن أدَّى هذه الصلوات يكون غالبًا خالي النفس من الكَسَل والرياء مُحِبًّا للعبادة.