Hadisai

Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنُؤَاخَذُ بِمَا عَمِلْنَا فِي الْجَاهِلِيَّةِ؟ قَالَ: «مَنْ أَحْسَنَ فِي الْإِسْلَامِ لَمْ يُؤَاخَذْ بِمَا عَمِلَ فِي الْجَاهِلِيَّةِ، وَمَنْ أَسَاءَ فِي الْإِسْلَامِ أُخِذَ بِالْأَوَّلِ وَالْآخِرِ».

Fassara

Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce: "Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe".

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar shiga Musulunci. Kuma cewa wanda ya musulunta kuma ya kyautata Musuluncinsa ya zama mai tsarkakewa mai gaskiya, to ba za’a yi masa hisabi da abinda ya aikata na sabo ba a lokacin Jahiliyya, Wanda ya munana a cikin Musulunci, da ya zama munafiki ko ya yi ridda ga Addininsa, za'a yi masa hisabi da abinda ya aikata a cikin kafirci, da kuma abinda ya aikata a cikin Musulunci.

Fa'idoji

  • Himmatuwar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kuma tsoronsu daga abinda ke tare da su na ayyukan Jahiliyya (da suka yi a baya).
  • Kwadaitarwa akan tabbata akan Musulunci.
  • Falalar shiga addinin Musulunci, kuma cewa shi yana kankare ayyukan da suka gabata.
  • Wanda ya yi ridda da munafiki za’a yi masa hisabi da dukkanin wani aikin da ya gabatar a lokacin Jahiliyya, haka ma kuma da dukkanin wani zinibin da ya aikata shi a cikin Musulunci.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبي صلى الله عليه وسلم فضل الدخول في الإسلام، وأن من أسلم وحسن إسلامه وكان مخلصًا صادقًا؛ فلا يحاسب بما عمل في الجاهلية من معاصي، ومن أساء في الإسلام بأن كان منافقًا أو ارتد عن دينه؛ حوسب بما عمل في الكفر وبما عمل في الإسلام.

  • اهتمام الصحابة رضوان الله عليهم وخوفهم مما كان منهم من الأعمال في الجاهلية.
  • الحث على الثبات على الإسلام.
  • فضل الدخول في الإسلام وأنه يكفر الأعمال السابقة.
  • المرتد والمنافق يُحاسَبُ بكلِّ عملٍ له سَبَقَ في الجاهلية، وبكل ذنب فَعله في الإسلام.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari