Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: تَوَضَّأَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَرَّةً مَرَّةً.
Fassara
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a sashin lokutansa idan zai yi alwala sai ya wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau ɗaiɗai, sai ya wanke fuska - daga [cikin wanke fuska] akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau ɗaiɗai, wannan shi ne gwargwadon wajibi.
Fa'idoji
- Wajibi a wanke gaɓɓai (shi ne) sau ɗaiɗai, abin da ya ƙaru, to, mustahabbi ne.
- Halaccin yin alwala sau ɗaiɗai a wasu lokuta
- Abin shar'anta wa a shafar kai (shi ne) sau ɗaiɗai.
Sharhi: العربية
كان النبيُّ صلى الله عليه وسلم في بعض أحيانه إذا توضأ غَسَلَ كلَّ عُضوٍ من أعضاء الوضوء مرة واحدة، فيَغْسِلُ الوجهَ -ومنه المضمضة والاستنشاق-، واليدين والرجلين مرة واحدة، وهذا هو القَدْرُ الواجب.
- الواجب في غَسْلِ الأعضاء مرة واحدة، وما زاد فهو مستحب.
- مشروعية الوضوء مَرّةً مرةً في بعض الأحيان.
- المشروع في مسح الرأس مرة واحدة.