Hadisai

Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi

Rubutun Larabci

عن قيس بن عاصم رضي الله عنه قال: أتيتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم أُريدُ الإسلامَ، فأَمَرَني أن أغتَسِلَ بماءٍ وسِدرٍ.

Fassara

Daga Ƙais ɗan Asim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya.

Sharhi

Ƙais ɗan Asim ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali yana son ya musulunta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya yi wanka da ruwa da (ganyan) bishiyar magarya; don kasancewa ganyanta ana amfani da shi a tsafta; don kuma abin da take da shi na ƙamshi mai daɗi.

Fa'idoji

  • Halaccin wankan kafiri a lokacin shigarsa Musulunci.
  • Darajar Musulunci da kulawarsa da jiki da rai gabaɗaya.
  • Cakuɗa ruwa da abubuwa masu tsarki ba ya fitar da shi daga tsarki.
  • Abubuwa na tsafta na zamani suna tsayawa a matsayin magarya, kamar sabulu da makamantansa.
Sharhi: العربية

جاء قيسُ بن عاصم إلى النبيِّ صلى الله عليه وسلم وهو يريد أن يُسْلِم، فأمرَه النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن يَغتسِلَ بماء وشَجَرِ السِدْر؛ لكون أوراقِهِِ تُستَعمل في التنظيف؛ ولِمَا له من رائحة طيبة.

  • مشروعيَّة اغتسال الكافر عند دخوله في الإسلام.
  • شرف الإسلام واهتمامه بالجسد والرُّوح معًا.
  • اختلاط الماء بالأشياء الطّاهرة لا يخرِجه عن الطّهوريَّة.
  • يقوم مقام السدر المنظفات الحديثة، كالصابون ونحوه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari