Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن سالم بن أبي الجَعْدِ قال: قال رجل: ليتني صَلَّيتُ فاسترحْتُ، فكأنّهم عابُوا ذلك عليه، فقال: سمعتُ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم يقول: «يا بلالُ، أقِمِ الصَّلاةَ، أرِحْنا بها».
Fassara
Daga Salim ɗan Abulja'ad ya ce: Wani mutum ya ce: Ina ma dai na yi sallah in huta, kamar cewa su (sauran mutanen) sun aibata masa hakan, sai ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita".
Sharhi
Wani mutum daga sahabbai ya ce: Ina ma na yi sallah in huta, kai ka ce waɗanda ke gefensa sun aibata hakan gare shi , sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Ya kai Bilal! ka kira sallah ka yi iƙamarta; don mu samu hutu da ita; saboda abin da ke cikinta na ganawa da Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma hutu ga rai da zuciya.
Fa'idoji
- Hutun zuciya yana kasancewa ne da yin sallah; saboda abin da ke cikinta na ganawa da Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Inkari a kan wanda ya ke yin nauyin (jiki) game da ibada.
- Wanda ya ba da wajibin da yake a kansa, ya kuɓutar da wuyayensa daga shi, hutu zai tabbata ta hakan gare shi da samun nutsuwa.
Sharhi: العربية
قال رجلٌ من الصحابة: ليتني صَليتُ فاستَرحتُ، فكأنَّ مَن حَوله عابُوا ذلك عليه، فقال: سمعتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم يقول: يا بلال! ارفع أذانَ الصلاةِ وأقِمْها؛ لنَستريحَ بها؛ وذلك لِمَا فيها من مناجاة لله تعالى، وراحة للروح والقلب.
- راحة القلب تكون بالصلاة؛ لما فيها من مناجاة الله تعالى.
- الإنكار على مَن تَثَاقَلَ عن العبادة.
- مَن أدَّى الواجِبَ الذي عليه، وأبرأ ذِمَّتَه منه، حَصَلتْ له بذلك راحةٌ وشعورٌ بالاطمئنان.