Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عنه سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ: «قَالَ اللهُ تَعَالَى: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ: {الْحَمْدُ لِلهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ}، قَالَ اللهُ تَعَالَى: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ: {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}، قَالَ: مَجَّدَنِي عَبْدِي، -وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي-، فَإِذَا قَالَ: {إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ}، قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ: {اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ، صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلا الضَّالِّينَ}، قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan bawa ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: bawaNa ya godemin, idan ya ce: {Mai kyauta a duniya mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: BawaNa ya yabeni, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakayya}, Zai ce: BawaNa ya girmamaNi, - wani lokaci kuma ya ce: bawaNa ya fawwala (al'amuransa) gareNi -, idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka kaɗai muke neman taimako}, sai Ya ce: Wannan tsakanina da tsakanin bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan ya ce: {ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanyar waɗanda Ka yi ni'ima a garesu ba waɗanda Ka yi fushi a kansu ba, ba kuma ɓatattu ba}, zai ce: Wannan ga bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa a hadisi Qudsi: Na raba Surar fatiha a sallah gida biyu tsakanina da tsakanin bawaNa, rabinta nawa ne, rabinta kuma nasane. Rabinta na farko: Godiya ne da yabo da girmama Allah, zan saka masa da mafificin sakamako. Rabinta na biyu: Ƙanƙar da kai ne da addu'a, zan amsa masa, kuma zan ba shi abin da ya roƙa. Idan mai sallah ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah zai ce: BawaNa ya gode min, idan ya ce; {Mai kyauta a duniya Mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah zai ce: BawaNa ya yabeni, sai ya yabeNi ya yi iƙirari da gamewar baiwa ga halittata, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakamako}, Allah zai ce: BawaNa ya girmamaNi, ita ce ɗaukaka mayalwaciya. Idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka ne kaɗai muke neman taimako}, Allah zai ce: Wannan tsakanina ne da tsakanin bawaNa. Ɓangare na farko daga wannan ayar shi ne: {Kai kaɗai muke bautawa} shi ne iƙirari da Allantakar Allah, da kuma amsawa ga yin bauta, da shi ne ɓangaren da yake ga Allah ya kare. Ɓangare na biyu daga ayar shi ga bawa ne: {Gareka ne kaɗai muke neman taimako} neman taimako daga Allah ne, da kuma alƙawarinSa na taimako. Idan ya ce: {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya* Hanyar waɗanda Ka yi ni'ima garesu, ba waɗanda Ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba}, Allah zai ce: Wannan ƙanƙar da kai ne da addu'a daga bawaNa, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, haƙiƙa na amsa addu'arsa.
Fa'idoji
- Girman sha'anin Fatiha haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - ya ambaceta (Sallah).
- Bayanin kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bawanSa, yayin da ya gode maSa sabo da godewarSa da yabonSa da girmamaShi, kuma Ya yi masa alƙawari zai ba shi abin da ya roƙa.
- Wannan surar mai girma ta ƙunshi godiya ga Allah, da ambaton makoma, da roƙon Allah, da tsarkake ibada gareShi, da roƙon shiriya zuwa hanya madaidaiciya, da gargaɗi a kan hanyoyin ƙarya ( bata ) .
- Jin wannan hadisin (ji irin na halarto da ma'anarsa) ga mai sallah - idan ya karanta fatiha - zai ƙara masa khushu'insa a sallarsa.
Sharhi: العربية
أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الله تعالى قال في الحديث القدسي: قسمت سورة الفاتحة في الصلاة بيني وبين عبدي نصفين، لي نصفُها، وله نصفُها. فنصفُها الأول: حمدٌ وثناءٌ وتمجيدٌ لله، أجزيه عليه خير الجزاء. ونصفُها الثاني: تَضَرُّعٌ ودعاء، أستجيب له وأعطيه ما سأل. فإذا قال المصلي: {الحمد لله رب العالمين}، قال الله: حمدني عبدي، وإذا قال: {الرحمن الرحيم}، قال الله: أثنى عليَّ عبدي فمدحني واعتراف لي بعموم الإنعام على خَلْقي، وإذا قال: {مالك يوم الدين}، قال الله: مَجَّدني عبدي، وهو الشرف الواسع. فإذا قال: {إياك نعبد وإياك نستعين}، قال الله: هذا بيني وبين عبدي. فالنصف الأول من هذه الآية لله وهو: (إياك نعبد) وهو اعتراف بالألوهية لله، والاستجابة بالعبادة، وبه ينتهي النصف الذي لله. والنصف الثاني من الآية وهو للعبد: (إياك نستعين) طلب العون من الله، ووعده بالإعانة. فإذا قال: {اهدنا الصراط المستقيم * صراط الذين أنعمت عليهم غير المغضوب عليهم ولا الضالين}، قال الله: هذا تضرُّع ودعاء من عبدي، ولعبدي ما سأل، وقد أجبتُ دعاءه.
- هذا الحديث مما يرويه النبي صلى الله عليه وسلم عن ربه، ويسمى بالحديث القدسي أو الإلهي، وهو الذي لفظه ومعناه من الله، غير أنه ليست فيه خصائص القرآن التي امتاز بها عما سواه، من التعبد بتلاوته والطهارة له والتحدي والإعجاز وغير ذلك.
- عظم شأن الفاتحة فقد سماها الله تعالى (الصلاة).
- بيان عناية الله تعالى بعبده، حيث مَدَحَه بسبب حَمْدِه وثنائِه وتمجيدِه، ووَعدَه أنْ يُعطيَه ما سأل.
- اشتملت هذه السورة الكريمة، على حمد الله، وذكر المعاد، ودعاء الله، وإخلاص العبادة له، وسؤال الهداية إلى الصراط المستقيم، والتحذير من مسالك الباطل.
- استشعار المصلي هذا الحديث -اذا قرأ الفاتحة- يَزيدُ مِن خشوعِه في الصلاة.