Hadisai

Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neIbnu Hibban ne ya Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَسْوَأُ النَّاسِ سَرَقَةً الَّذِي يَسْرِقُ صَلَاتَهُ» قَالَ: وَكَيْفَ يَسْرِقُ صَلَاتَهُ؟ قال: «لَا يُتِمُّ رُكُوعَهَا، وَلَا سُجُودَهَا».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".

Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mafi tsananin mutane muni a sata shi ne wanda yake satar sallarsa; hakan ya kasance ne domin karɓar dukiyar wani wataƙila zai iya amfani da ita a duniya, saɓanin wannan satar, domin ya saci haƙƙin kansa na sakamako da lada, suka ce: Ya Manzon Allah, ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: Ba ya cika ruku'unta kuma ba ya cika sujjadarta; hakan yana nufin ya yi gaggwa a ruku'u da sujjada, ba zai zo da su ba a kan cikkakkiyar fuskar su ba.

Fa'idoji

  • Muhimmancin kyautata sallah da zuwa da rukunanta da nutsuwa da ƙanƙar da kai.
  • Siffanta wanda ba ya cika ruku'unsa da sujjadarsa da cewa shi ɓarawo ne; kyamatar hakan ne gami da faɗakarwa a kan haramcinsa.
  • Wajabcin cika ruku'u da sujjada a sallah da daidaito a cikinsu.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ أشدَّ الناسِ قُبْحًا في السَّرِقَة الذي يَسْرِقُ مِن صلاتِه؛ وذلك لأنَّ أَخْذَ مالِ الغيرِ ربما ينتفع به في الدنيا، بخلاف هذا السارق، فإنه سَرَقَ حقَّ نفسِه مِن الثواب والأجر، قالوا: يا رسول الله، وكيف يسرق من صلاته؟ قال: لا يتم ركوعها ولا سجودها؛ وذلك بأنْ يستعجل في الركوع والسجود، فلا يأتي بهما على الوجه الأكمل.

  • أهمية إحسان الصلاة والإتيان بأركانها بطمأنينة وخشوع.
  • وصف مَن لا يتم ركوعه وسجوده بأنه سارقٌ تنفيرٌ عن ذلك، وتنبيهٌ على تحريمِه.
  • وجوب إتمام الركوع والسجود في الصلاة والاعتدال منهما.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari