Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ سَفِينَةَ رَضيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُغَسِّلُهُ الصَّاعُ مِنَ المَاءِ مِنَ الجَنَابَةِ، وَيُوَضِّئُهُ المُدُّ.

Fassara

Daga Safina - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wankan tsarki da sa’i ɗaya, kuma yana alwala da mudun Nabiy ɗaya. Sa'i: Mudun Nabiy haɗu ne, mudun Nabiy kuma: Gwargwadan cikin tafuka biyu na mutum madaidaicin halitta.

Fa'idoji

  • Halaccin tattali a ruwan alwala da wanka, da rashin ɓarna, koda ruwan ya kasance mai sauƙin samu ne.
  • An so ƙaranta ruwan alwala da wanka gwargwadan buƙata, kuma wannan ita ce shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Abin nufi cikawa a alwala da wanka tare da kula da sunnoni da ladubba ba tare da ɓarna ko ƙwauro ba, kuma a kiyaye lokaci da yawan ruwan da ƙarancinsa da wanin hakan.
  • Ana anbaton janaba ga dukkan wanda ya fitar da maniyyi ko ya yi jima'i, kuma an anbaceta da hakan dan mai ita yana nisantar sallah da ibadu har sai ya tsarkaka daga gareta.
  • Sa'i: wani abin awo ne sananne, abin nufi da shi sa'in Annabi, awonsa ya kai nauyi (480) na alkama mai kyau, a lita kuma (lita 3).
  • Mudun Nabiy: Awo ne na shari'a, shi kuma cikin tafuka biyu ne na mutum madaidaici idan ya cikasu ya miƙe hannunsa da su. Mudun Nabiy shi ne ɗaya bisa huɗu na sa'i da haɗuwar masana fiƙihu, gwargwadansa ML (750).
Sharhi: العربية

كان النبي صلى الله عليه وسلم يغتسل من الجنابة بالصاع، ويتوضأ بالمد، والصاع: أربعة أمداد، والمد: مِقْدار مِلء كفَّي إنسانٍ مُعتدلِ الخِلْقة.

  • مشروعية الاقتصاد في ماء الوضوء والغسل، وعدم الإسراف ولو كان الماء مُتيسّرًا.
  • استحباب التقليل في ماء الوضوء والغسل بقدر الحاجة، وأن هذا هو هدي النبي صلى الله عليه وسلم.
  • المقصود الاستيفاء في الوضوء والغسل مع مراعاة السنن والآداب بلا إسراف ولا تقتير، ويراعى الوقت وكثرة الماء وقلته وغير ذلك.
  • تطلق الجنابة على كل من أنزل المنيَّ أو جامع، وسميت بذلك لاجتناب صاحبها الصلاة والعبادات حتى يطهر منها.
  • الصاع: مكيال معروف، والمراد به الصاع النبوي، ويبلغ وزنه (480) مثقالًا من البر الجيد، وباللتر (3 لترات).
  • المد: وحدةُ كيلٍ شرعية، وهي ملء كفي الإنسان المعتدل إذا ملأهما ومَدَّ يدَه بهما، والمد ربع الصاع باتفاق الفقهاء، ومقداره (750) ملل.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari