Hadisai

Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ سَعْدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنْتُ أَرَى رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ، وَعَنْ يَسَارِهِ، حَتَّى أَرَى بَيَاضَ خَدِّهِ.

Fassara

Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa.

Sharhi

Sa'ad Ibnu Abi Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana ganin farin kundukukin (kumatun) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda tsananin waiwayensa idan zai sallame daga sallarsa a damansa a sallamar farko, haka a hagunsa a (sallama) ta biyu.

Fa'idoji

  • Halaccin kai matuƙa a cikin waiwaye zuwa ɓangaren dama da kuma ɓangaren hagu.
  • Halaccin sallama biyu zuwa dama da hagu.
  • Nawawi ya ce: Da a ce zai yi sallama biyu a damarsa ko a hagunsa ko ta ɓangaren fuskarsa, ko ta farkon a hagunsa, ta biyun kuma a damansa sallarsa ta inganta kuma sallama biyun ta tabbata, sai dai ya rasa falala ta yadda ake yinsu .
Sharhi: العربية

أخبر سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه أنه كان يرى بياض خدِّ النبي صلى الله عليه وسلم من شدة التفاتِهِ إذا سلَّم من صلاته عن يمينه للتسليمة الأولى، وعن يساره للثانية.

  • مشروعية المبالغة في الالتفات إلى جهة اليمين وإلى جهة اليسار.
  • مشروعية التسليمتين إلى اليمين واليسار.
  • قال النووي: ولو سلَّم التسليمتين عن يمينه أو عن يساره أو تلقاء وجهه أو الأولى عن يساره والثانية عن يمينه صحت صلاته وحصلت التسليمتان، ولكن فاته الفضيلة في كيفيتهما.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari