Hadisai

A kwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu, akwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu" sannan ana uku ya ce: "Ga wanda ya so

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مُغَفَّلٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: «بَيْنَ كُلِّ أَذَانَيْنِ صَلَاةٌ، بَيْنَ كُلِّ أَذَانَيْنِ صَلَاةٌ» ثُمَّ قَالَ فِي الثَّالِثَةِ: «لِمَنْ شَاءَ».

Fassara

Daga Abdullahi dan Mugaffal - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "A kwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu, akwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu" sannan ana uku ya ce: "Ga wanda ya so".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sallar nafila tsakanin kowanne kiran sallah da iƙama, kuma ya maimaita hakan sau uku, kuma ya bada bayani ana ukun cewa hakan mustahabbi ne ga wanda ya yi nufin yin sallah.

Fa'idoji

  • An so sallah tsakanin kiran sallah da iƙama.
  • Shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a maimaita magana, hakan dan jiyarwa da ƙarfafawa ga muhimmnacin abinda yake faɗa.
  • Abin nufi da kiran sallah biyu: Kiran sallah da iƙama, kuma ya anbace su da (lafazin) (Kiran sallah biyu) dan rinjayarwa, kamar wata biyu (Rana da wata) da Umar biyu (Abubakar da Umar).
  • Kiran sallah shi ne sanar da shigar lokaci, iƙama kuma ita ce sanar da halartar yin sallah.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ بَيْنَ كلِّ أذانٍ وإقامةٍ صلاةُ نافلةٍ، وكرَّر ذلك ثلاثًا، وأخبر في الثالثة أن ذلك مُستحبٌّ لِمَن أراد أن يصلي.

  • استحباب الصلاة بين الأذان والإقامة.
  • هدي النبي صلى الله عليه وسلم في تكرار القول، وذلك إسماعًا وتأكيدًا لأهمية ما يقول.
  • المراد بالأذانين: الأذان والإقامة، وأطلق عليهما (الأذانَين) تغليبًا، كالقمرين (الشمس والقمر) والعُمَرَيْن (أبي بكر وعمر).
  • الأذان إعلام بدخول الوقت، والإقامة إعلام بحضور فعل الصلاة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari