Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi
Rubutun Larabci
عن أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيَّ رَضِيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهُ صلَّى اللهُ عليهِ وَسَلَّم: «لَقِّنُوا مَوْتَاكُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ».
Fassara
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah»
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa kan mu faɗi kuma mu maimaita kalamr Tauhidi "La'ilaha illallahu" a wurin wanda fizgar mutuwa ta zo masa har sai ya faɗeta, dan ta zama ƙarshen maganarsa.
Fa'idoji
- An so yi wa wanda mutuwa ta halarto masa talƙini.
- An karhanta yawaita yin talƙini ga wanda mutuwa ta halarto masa, da kuma nacewa a kansa idan ya karɓi talƙinin, ko an fahimci hakan daga gare shi; dan kada ya takura masa sai ya furta abin da bai dace ba.
- Nawawi ya ce: Idan ya faɗeta sau ɗaya to kada ya maimaita masa saidai idan ya yi wata maganar daban a bayansa, sai asake bijiro masa da ita dan ta zama ita ce ƙarshen zancensa.
- Hadisin ya ƙunshi halartar wurin da wanda mutuwa ta halarto masa dan tinatar da shi da kuma yi debe masa kewa da rintse idanuwansa da kuma tsayuwa da haƙƙoƙinsa.
- Rashin halaccin yin talƙini bayan mutuwa da wurin ƙabari bayan an binne; saboda rashin aikata hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sharhi: العربية
يحثُّ النبي صلى الله عليه وسلم: أن نقول ونردد كلمة التوحيد "لا إله إلا الله" عند مَن حضرته نزعات الموت حتى يقولها، لتكون آخر كلامهم.
- استحباب التلقين لمن حضره الموت.
- كراهة الإكثار على المحتضر من التلقين، والإلحاح عليه إذا هو تلقنها، أو فهم عنه ذلك؛ لكي لا يُضجِرَه فينطق بما لا يليق.
- قال النووي: وإذا قاله مرة لا يكرر عليه إلا أن يتكلم بعده بكلام آخر، فيُعاد التعريض به ليكون آخر كلامه.
- يتضمن الحديث الحضور عند المحتضر لتذكيره وتأنيسه وإغماض عينيه والقيام بحقوقه.
- عدم مشروعية التلقين بعد الموت وعند القبر بعد الدفن؛ لعدم فعل النبي صلى الله عليه وسلم ذلك.