Hadisai

Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan ne ta jimillar hanyoyinsaAbu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi

Rubutun Larabci

عن سعد بن عبادة رضي الله عنه أنه قال: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّ أُمَّ سَعْدٍ مَاتَتْ، فَأَيُّ الصَّدَقَةِ أَفْضَلُ؟، قَالَ: «الْمَاءُ»، قَالَ: فَحَفَرَ بِئْرًا، وَقَالَ: هَذِهِ لِأُمِّ سَعْدٍ.

Fassara

Daga Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce.

Sharhi

Mahaifiyar Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - ta rasu, sai ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafificin nau'ikan sadaka dan ya yi sadaka dashi ga mahaifiyarsa? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ba shi labarin: Cewa mafificiyar sadaka ita ce ruwa, sai ya haƙa wata rijiya ya sanyata sadaka ga mahaifiyarsa.

Fa'idoji

  • Bayanin cewa ruwa yana daga mafificin nau'ikan sadaka.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunawa da Sa'ad zuwa ga sadakar ruwa; domin shi ya fi gamewar anfani a cikin al'amuran addini da duniya, kuma saboda tsananin zafi da buƙata da ƙarancin ruwa.
  • Nuni akan ladan sadaka yana zuwa ga mamata.
  • Biyayyar Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - ga mahaifiyarsa - Allah Ya yarda da su -.
Sharhi: العربية

تُوُفِّيَتْ أُمُّ سَعْدِ بن عبادة رضي الله عنه، فسألَ النبيَّ صلى الله عليه وسلم عن أفضل أنواع الصدقة لِيتصدَّقَ به عن أُمِّه؟ فأخبره صلى الله عليه وسلم: أنّ أفضلَ الصدقة هي الماء، فَحَفَرَ بئرًا وجَعَلَها صدقةً لأمِّهِ.

  • بيان أنَّ الماء من أفضل أنواع الصدقة.
  • أرشد النبيُّ صلى الله عليه وسلم سعدًا إلى صدقة الماء؛ لأنه أعم نفعًا في الأمور الدينية والدنيوية، ولِشدّة الحَرّ والحاجة وقلة الماء.
  • الدلالة على أنّ أجورَ الصدقات تصل إلى الأموات.
  • بر سعد بن عبادة رضي الله عنه بوالدته رضي الله عنهما.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari