Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي الْجَعْدِ الضَّمْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ، وَكَانَتْ لَهُ صُحْبَةٌ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ تَرَكَ ثَلَاثَ جُمَعٍ تَهَاوُنًا بِهَا طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قَلْبِهِ».
Fassara
Daga Abul Ja'ad al-Damri - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance sahabi ne, cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a, kuma wanda ya bar sallar Juma'a sau uku dan sakaci da kasawa ba tare da wani uzuri ba Allah zai rufe zuciyarsa ta hanyar hana isar alheri gare shi .
Fa'idoji
- Ibnul Munzir ya hakaito Ijma'i akan cewa sallar Juma'a farilla ce ta aini (wato ta hau kan kowa).
- Narko akan wanda ya bar Juma'a dan sakaci shi ne Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa.
- Wanda ya bar Juma'a dan wani uzuri to shi ba ya shiga cikin narkon.
- Al-Shaukani ya ce: Faɗinsa: (Juma'o'i uku), yana ɗaukar cewa ana nufin faruwar barin kai tsaye daidai ne Juma'o'in a jere ne ko sun rarrabu, hatta da a ce duk shekara zai bar Juma'a ɗaya da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi yumƙi akan zuciyarsa bayan ta uku shi ne zahirin hadisin, kuma zai iya ɗaukar cewa ana nufin Juma'o'i ukun a jere.
Sharhi: العربية
حَذَّر النبي صلى الله عليه وسلم من ترك صلاة الجمعة، وأن من ترك صلاة الجمعة ثلاث مرات تساهلًا وتقصيرًا من غير عذر خَتَم وغَطَّى الله على قلبه بمنع إيصال الخير إليه.
- حكى ابن المنذر الإجماع على أن صلاة الجمعة فرض عين.
- الوعيد لمن ترك الجمعة تساهلًا بأن يطبع الله على قلبه.
- من ترك الجمعة لعذر فلا يدخل في الوعيد.
- قال الشوكاني: قوله: (ثلاث جمع)، يحتمل أن يراد حصول الترك مطلقًا سواء توالت الجمعات أو تفرّقت، حتى لو ترك في كل سنة جمعة لطبع الله تعالى على قلبه بعد الثالثة وهو ظاهر الحديث، ويحتمل أن يراد ثلاث جمع متوالية.