Hadisai

Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ لِبِلاَلٍ عِنْدَ صَلاَةِ الفَجْرِ: «يَا بِلاَلُ، حَدِّثْنِي بِأَرْجَى عَمَلٍ عَمِلْتَهُ فِي الإِسْلاَمِ، فَإِنِّي سَمِعْتُ دَفَّ نَعْلَيْكَ بَيْنَ يَدَيَّ فِي الجَنَّةِ» قَالَ: مَا عَمِلْتُ عَمَلًا أَرْجَى عِنْدِي أَنِّي لَمْ أَتَطَهَّرْ طَهُورًا، فِي سَاعَةِ لَيْلٍ أَوْ نَهَارٍ، إِلَّا صَلَّيْتُ بِذَلِكَ الطُّهُورِ مَا كُتِبَ لِي أَنْ أُصَلِّيَ.

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce wa Bilal yayin sallar Asuba: "Ya kai Bilal, ka bani labarin mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin musulunci, domin ni na ji takun takalmanka a gabana a cikin aljanna" Ya ce: Ban taɓa aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a gurina sai dai cewa bana yin wata alwala a lokacin dare ko rana, sai na sallaci abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin mafarki ya gan shi a cikin aljanna, sai ya cewa Bilal Ibnu Rabah: Bani labarin mafi kwaɗayin aikin nafilar da ka aikata shi a cikin Musulunci? Domin ni na ji ƙarar takalmanka a hankali lokacin da kake motsasu kana tafiya a gabana a cikin aljanna. Bilal ya ce: Ban aikata wani aiki ba mafi kwaɗayi a wurina sai dai cewa ni ban taɓa yin kari (hadasi) ba da daddare ko da rana ba face sa na yi alwala, sannan na yi sallah saboda Ubangijina, ta nafilfili kai tsaye abin da aka rubuta mini in sallata da wannan alwalar

Fa'idoji

  • Falalar aikin da Bilal - Allah Ya yarda da shi - ya yi nuni a kansa, shine sallah a duk lokacin da mutum ya yi tsarki ya yi alwala, kuma shi yana daga cikn mafi kwaɗayin ayyuka kuma sababi na shiga aljanna.
  • An so yin sallah bayan kowace alwala.
  • Tambayar (mutum) wanda ake koyi da shi ko mai tarbiyya game da aikin almajirinsa; dan ya kwaɗaitar da shi akan tabbata a kansa idan ya kasance mai kyau ne, inba haka ba to sai ya hana shi.
  • Shaidar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa Bilal - Allah Ya yarda da shi - da cewa shi yana daga cikin 'yan aljanna.
  • Wannan tambayar a lokacin sallar Asuba ce, a cikin wannan akwai nuni cewa hakan ya faru ne a cikin mafarki daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma mafarkin Annabawa gaskiya ne.
Sharhi: العربية

رأى النبي صلى الله عليه وسلم في المنام أنه في الجنة، فقال لبلال بن رباح: أخبرني بأرجى عملِ تطوعٍ عملته في الإسلام؟ فإني سمعت صوتًا خفيفًا لنعليك عند تحريكهما بالمشي أمامي في الجنة. قال بلال: ما عملت عملًا أرجى عندي أني لم أحدث في ساعة ليل أو نهار إلا وتوضأت، ثم صليت لربي بذلك الوضوء من النوافل المطلقة ما كتب لي أن أصلي.

  • فضل العمل الذي دل عليه بلال رضي الله عنه، ألا وهو الصلاة كلما تطهر وتوضأ، وأنه من أرجى الأعمال وسبب لدخول الجنة.
  • استحباب الصلاة بعد كل وضوء.
  • سؤال القدوة أو المربي عن عمل تلميذه؛ ليحضَّه على الثبات عليه إن كان حسنًا، وإلا فينهاه.
  • شهادة من النبي صلى الله عليه وسلم لبلال رضي الله عنه بأنه من أهل الجنة.
  • هذا السؤال عند صلاة الفجر، وفي هذا إشارة إلى أن ذلك وقع في رؤيا منام منه صلى الله عليه وسلم، ورؤيا الأنبياء حق.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari