Hadisai

‌Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin mafi alherin zancen halitta (suna yawaita karatun Alƙur'ani), zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga abin da aka harba,

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: إِذَا حَدَّثْتُكُمْ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَلَأَنْ أَخِرَّ مِنَ السَّمَاءِ أَحَبُّ إِلَيَّ مِنْ أَنْ أَكْذِبَ عَلَيْهِ، وَإِذَا حَدَّثْتُكُمْ فِيمَا بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ فَإِنَّ الحَرْبَ خَدْعَةٌ، سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «يَأْتِي فِي آخِرِ الزَّمَانِ قَوْمٌ حُدَثَاءُ الأَسْنَانِ سُفَهَاءُ الأَحْلاَمِ، يَقُولُونَ مِنْ خَيْرِ قَوْلِ البَرِيَّةِ، يَمْرُقُونَ مِنَ الإِسْلاَمِ كَمَا يَمْرُقُ السَّهْمُ مِنَ الرَّمِيَّةِ، لاَ يُجَاوِزُ إِيمَانُهُمْ حَنَاجِرَهُمْ، فَأَيْنَمَا لَقِيتُمُوهُمْ فَاقْتُلُوهُمْ، فَإِنَّ قَتْلَهُمْ أَجْرٌ لِمَنْ قَتَلَهُمْ يَوْمَ القِيَامَةِ».

Fassara

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -: Idan na zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ace in faɗo daga sama shi ya fi soyuwa gareni daga in yi masa (Annabi) ƙarya, idan na zantar da ku a abinda yake tsakanina da ku to lallai yaƙi ɗan yaudara ne, na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «‌Wasu mutane zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru masu raunin hankula, suna faɗin mafi alherin zancen halitta (suna yawaita karatun Alƙur'ani), zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga abin da aka harba, imaninsu ba zai ƙetare maƙogwaransu ba, a duk inda kuka gamu da su to ku kashesu, domin kashesu lada ne ga wanda ya kashesu a ranar alƙiyama».

Sharhi

Sarkin musulmai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa idan kuka ji ni ina zantar da wani hadisi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lallai cewa ni banayin alkunya bana yin jirwaye mai kama da wanka kuma bana yin tauriyya, kawai ina magana ne ɓaro-ɓaro, kuma a ce in faɗo daga sama shi ya fi sauƙi a gurina daga in zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ina yi masa ƙarya, idan na yi magana a abinda ke tsakanina da mutane to lallai cewa yaƙi ɗan yaudara ne, saboda haka zan iyayin alkunya ko in yi jirwaye mai kama da wanka ko in yi tauriyya, haƙiƙa na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Wasu matasa zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru, masu raunin hankula, suna faɗin (magana daga) Alƙur'ani kuma suna yawaita karanta shi, zasu fita daga Musulunci kuma su ƙetare iyakokinsa kamar yadda kibiya take fita daga abinda aka harba, imaninsu ba ya wuce maƙogwaransu, a duk inda kuka haɗu da su to ku kashesu, domin cewa kashesu lada ne ga wanda ya kashesu a ranar alƙiyama.

Fa'idoji

  • Bayanin wani abu daga cikin siffofin Khawarij.
  • A cikin hadisin akwai alama daga alamomin Annabta, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin abinda zai faru a bayansa, sai ya faru kamar yadda ya bada labarin shi.
  • Halaccin yin tauriyya da jirwaye mai kama da wanka a cikin yaƙi, yaudara a cikin yaƙi tana kasancewa ne ta hanyar yin tauriyya, kuma tana kasancewa ta hanyar bazata, da makamancinsu, ba tare da warware alƙawari ba ko (warware) amintarwa ba, saboda zuwan hani akan hakan.
  • Nawawi ya ce akan (ma'anar) (Suna faɗa daga mafi alherin zancen talikai) Ma'anarsa: A zahirin al'amari kamar faɗinsu: Babu wani hukunci sai na Allah, da makamancinsa daga kiransu zuwa Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  • Ibnu Hajar ya ce a cikin faɗinsa (Imaninsu ba ya ƙetare maƙogwaransu): Abin nufi cewa imani bai tabbata a cikin zukatansu ba; domin dukkan abinda ya tsaya a maƙogwaro bai ƙetare shi ba to ba ya kaiwa zuciya.
  • Alƙali ya ce: Malamai sun yi ijma'i akan cewa Kahawarij da makamantansu cikin 'yan bidi'a da tawaye a duk lokacin da suka yi wa shugaba tawaye suka saɓa ra'ayin jama'a suka raba kawunan mutane to ya wajaba a yaƙesu bayan an yi musu gargaɗi, an gabatar da uzuri garesu.
Sharhi: العربية

أخبر أمير المؤمنين علي بن أبي طالب رضي الله عنه أنه إذا سمعتموني أحدّث عن النبي صلى الله عليه وسلم فإني لا أكنّي ولا أُعرّض ولا أواري، وإنما أصرّح، ولأن أقع من السماء أيسر عندي وأخف من أن أحدث عن رسول الله صلى الله عليه وسلم وأنا أكذب عليه، وإذا حدثت فيما بيني وبين الناس فإنما الحرب خدعة، فقد أكني أو أعرّض أو أواري، وقد سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: يأتي في آخر الزمان شباب صغار السن، ضعاف العقول، يقولون من القرآن ويكثرون قراءته، يخرجون من الإسلام ويتعدّون حدوده كما يخرج السهم من الرمية، لا يجاوز إيمانهم حناجرهم، فأينما لقيتموهم فاقتلوهم، فإن قتلهم أجر لمن قتلهم يوم القيامة.

  • بيان شيء من صفات الخوارج.
  • في الحديث علمٌ من أعلام النبوة، حيث أخبر النبي صلى الله عليه وسلم بما سيقع بعده في أمته، فوقع كما أخبر به.
  • جواز التّورية والتعريض في الحرب، والخديعة في الحرب تكون بالتورية، وتكون بالكمين، ونحوهما، دون نقض العهد والأمان، لورود النهي عن ذلك.
  • قال النووي على (يقولون من خير قول البرية) ‏معناه: في ظاهر الأمر كقولهم: لا حكم إلا لله، ونظائره من دعائهم إلى كتاب الله تعالى.
  • قال ابن حجر في قوله (لاَ يُجَاوِزُ إِيمَانُهُمْ حَنَاجِرَهُمْ): المراد أن الإيمان لم يرسخ في قلوبهم؛ لأن ما وقف عند الحلقوم فلم يتجاوزه لا يصل إلى القلب.
  • قال القاضي: أجمع العلماء على أن الخوارج وأشباههم من أهل البدع والبغي متى خرجوا على الإمام وخالفوا رأي الجماعة وشقوا العصا وجب قتالهم بعد إنذارهم، والاعتذار إليهم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari