Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لاَ يَزَالُ قَلْبُ الكَبِيرِ شَابًّا فِي اثْنَتَيْنِ: فِي حُبِّ الدُّنْيَا وَطُولِ الأَمَلِ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dattijo yana girma jikinsa yana rauni, sai dai zuciyarsa budurwa ce akan son abubuwa biyu: Na farko: Son duniya da yawan dukiya. Na biyu: Tsawon rayuwa da shekaru da buri.
Fa'idoji
- Bayanin abinda aka halicci mutum a kansa, shi ne son duniya da tsawon buri.
- Nuni akan zargin yawan buri, da kwaɗayi akan tara dukiya, hakan yana hukunta tanadi ga mutuwa da falalar sadaka ga mawadaci, da kamewa ga talaka.
- Mafi soyuwar abubuwa ga ɗan Adam shi ne ransa, shi mai kwaɗayi ne a akan wanzuwarsa, saboda haka sai ya so tsawon rayuwa, kuma ya so dukiya; domin cewa shi yana daga mafi girman sabubba a dawwamar lafiya da jin daɗi, a duk lokacin da ya ji kusancin ƙarewar hakan sai sonsa gare shi ya tsananta, da kuma kwaɗayinsa a kan dawwamarsa.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن الشيخ يَكبُر ويضعُف جسمُه ولكن قلبُه شابٌّ على حب اثنتين: الأولى: حب الدنيا بكثرة المال. والثانية: طول الحياة والعمر والعيش والأمل.
- بيان ما جُبِل عليه الإنسان، وهو حب الدنيا وطول الأمل.
- الإشارة إلى ذم طول الأمل، والحرص على جمع المال، وذلك يقتضي التأهُّب للموت وفضل الصدقة للغني، والتعفُّف للفقير.
- أحب الأشياء إلى ابن آدم هي نفسه، فهو راغب في بقائها، فأحب لذلك طول العمر، وأحب المال؛ لأنه من أعظم الأسباب في دوام الصحة والمتعة، فكلما أحس بقرب نفاد ذلك اشتد حبه له، ورغبته في دوامه.