Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِيَّاكُمْ وَمُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ، فَإِنَّمَا مَثَلُ مُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ كَقَوْمٍ نَزَلُوا فِي بَطْنِ وَادٍ، فَجَاءَ ذَا بِعُودٍ، وَجَاءَ ذَا بِعُودٍ، حَتَّى أَنْضَجُوا خُبْزَتَهُمْ، وَإِنَّ مُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ مَتَى يُؤْخَذْ بِهَا صَاحِبُهَا تُهْلِكْهُ».
Fassara
Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Na haneku da ƙananan zunibai, kaɗai misalin ƙananan zunubai kamar mutane ne da suka sauka a cikin wani kwari, sai wannan ya zo da ice, wannan ma ya zo da ice, har suka sa gurasarsu ta nuna, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu saboda su zasu halaka shi».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga sakaci a aikata ƙananan zunubai, da kuma yawaitasu domin cewa su idan sun taru zasu halakar, kuma ya buga misali akan hakan da wasu mutanen da suka sauka a cikin wani kwari, sai kowanne daga cikinsu ya zo da ita ce ƙarami, har sai da suka sa gurasarsu ta nuna saboda taruwar abinda suka tara na itatuwan, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu da su bai tuba daga garesu ba ko kuma Allah bai yi masa afuwa ba to zasu halaka shi.
Fa'idoji
- Shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a buga misalai dan kusanto da fahimta da kuma ƙara bayani.
- Gargaɗarwa daga ƙananan zunubai waɗanda ake wulaƙantar da su, da kuma kwaɗaitarwa akan gaggawar kankare su.
- Ƙanana zunubai suna ɗaukar ma'anoni: Na farko: Abinda bawa yake aikata shi cikin zunubai, yana mai ɗimuwar cewa shi ƙarami ne, alhali shi yana cikin manyan zunubai a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -. Na biyu: Abinda bawa yake aikata shi daga ƙananan zunubai ba tare da kulawa da su ba, sai waɗannan ƙananan zunuban su taru a kansa har sai sun halaka shi. Na uku: Abinda bawa yake aikata shi na ƙananan zunubai, ba ya kulawa da su, sai su zama sababi dan afkawarsa a cikin manyan zunubai masu halakarwa.
Sharhi: العربية
حذر النبي صلى الله عليه وسلم من التساهل في فعل صغائر الذنوب، والإكثار منها فإنها تهلك بمجموعها، وضرب مثلًا على ذلك بقوم نزلوا في بطن واد، فجاء كل واحد منهم بعُوْد صغير، حتى أنضجوا خُبزتهم بمجموع ما جمعوا من العيدان، وإن محقرات الذنوب متى يؤخذ بها صاحبها ولم يتب منها أو يعفو الله عنه أهلكته.
- هدي النبي صلى الله عليه وسلم في ضرب الأمثال تقريبًا للفهم وزيادة في البيان.
- التحذير من صغائر الذنوب المستحقرة، والحث على البِدار في تكفيرها.
- محقرات الذنوب تحتمل معانيًا: الأول: ما يفعله العبد من الذنوب، متوهمًا أنه من صغارها، وهو من كبار الذنوب عند الله تعالى، والثاني: ما يفعله العبد من صغائر الذنوب، دون مبالاة بها، ولا توبة منها، فتجتمع عليه هذه الصغائر حتى تهلكه، والثالث: ما يفعله العبد من صغائر الذنوب، لا يبالي بها، فتكون سببًا لوقوعه في الكبائر المهلكة.