Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللهَ يَرْضَى لَكُمْ ثَلَاثًا، وَيَكْرَهُ لَكُمْ ثَلَاثًا، فَيَرْضَى لَكُمْ: أَنْ تَعْبُدُوهُ، وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَأَنْ تَعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا، وَيَكْرَهُ لَكُمْ: قِيلَ وَقَالَ، وَكَثْرَةَ السُّؤَالِ، وَإِضَاعَةِ الْمَالِ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya yardar muku da abubuwa uku, kuma Yana ƙin abubuwa uku a gareku, Yana yardar muku: Ku bauta maSa, kada ku haɗa shi da wani abu a bauta, kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gabaɗaya kada ku rarraba. Kuma yana ƙi muku: Ƙila wa ƙala, da yawan roƙo, da kuma tozartar da dukiya».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Yana son ɗabi'u uku daga bayinSa, kuma Yana ƙin abubuwa uku daga gare su, Yana so daga garesu: Su kaɗaita Shi da bauta kada su taranya wani abu a cikin bautarSa, kuma su yi riƙo da alƙawarin Allah da kuma Alƙur'ani da sunnar AnnabinSa bakiɗaya, kada su rarraba daga jama'ar musulmai. Kuma yana ƙi musu: zance mara anfani da yasasshiyar magana a cikin abinda babu ruwansu, da kuma tambayar abinda bai afku ba, ko roƙon mutane dukiyoyinsu, da kuma abinda ke hannunsu, da kuma abinda ba'a buƙatarsa, da tozarta dukiya da bada ita ba ta fuskar shari'a ba, da kuma bijiro da ita ga abinda zai lalata ta.
Fa'idoji
- Allah Yana son ikhlasi daga bayinSa a cikin bautarSa, kuma yana ƙin kafirci daga bayinsa.
- Kwaɗaitarwa akan riƙo da igiyar Allah - Maɗaukakin sarki -; saboda abinda ke cikinsa ha haɗuwar kai.
- Kwaɗaitarwa akan jama'a, da kuma umarni da lazimtarta da hada kai, da kuma hani daga kishiyarta na rarrabuwa da kuma saɓani.
- Hani daga yawan zancen da ba shi da amfani; domin idan ya kasance abin halattawa ne to a cikinsa akwai bata lokaci, idan kuma haramun ne to a cikinsa akwai yawan zunubi.
- Barin kutsawa a cikin labarun mutane da kuma bibiyar halayensu da kwaikwayar maganganunsu da kuma ayyukansu.
- Hani daga yawan roƙon dukiyoyin mutane.
- Haramta lalatar da dukiya, da kuma kwaɗaitarwa akan kiyayeta a abinda yake anfanarwa.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن الله يحب من عباده ثلاث خصال، ويكره منهم ثلاثًا، فيحب منهم: أن يوحدوه ولا يشركوا به شيئًا، وأن يعتصموا بعهد الله والقرآن وسنة نبيه جميعًا، ولا يتفرقوا عن جماعة المسلمين. ويكره لهم: اللغو وفضول الكلام فيما لا يعنيهم، والسؤال عما لم يقع، أو سؤال الناس أموالهم، وما في أيديهم، وما لم تدعو إليه حاجة، وإضاعة المال وصرفه في غير وجوهه الشرعية، وتعريضه للتلف.
- يحب الله تعالى من عباده الإخلاص في عبادته، ويبغض الكفر به.
- الحض على الاعتصام والتمسك بحبل الله تعالى؛ لما فيه من اجتماع وائتلاف.
- الحث على الجماعة، والأمر بلزومها وتوحيد صفوفها، والنهي عن ضدها من التفرق والاختلاف.
- النهي عن كثرة الكلام بما لا يعني؛ لأنه إن كان مباحًا ففيه إضاعة الوقت، وإن كان حرامًا ففيه كثرة المآثم.
- ترك الخوض في أخبار الناس وتتبع أحوالهم وحكاية أقوالهم وأفعالهم.
- النهي عن كثرة السؤال لأموال الناس.
- تحريم إضاعة المال، والحث على المحافظة عليه فيما ينفع.