Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: يُؤْذِينِي ابْنُ آدَمَ يَسُبُّ الدَّهْرَ وَأَنَا الدَّهْرُ، بِيَدِي الأَمْرُ أُقَلِّبُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Ɗan Adam ya cutar da Ni yana zagin zamani alhali Nine zamani, al'amari yana hannunNa iNa jujjuya dare da rana».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Mutumin da yake zagin zamani a lokacin saukar masifu da abubuwan ƙi yana cuta ta kuma yana tauyeNi; domin cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne Mai jujjuya al'amura Shi kaɗai, kuma Mai sarrafa abinda yake faruwa; to aibata zamani aibata Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, zamani kuwa kawai shi halitta ne abin horewa, abubuwa suna gudana ne a cikinsa da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Fa'idoji
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu abubuwan da Alƙur’ani ya keɓanta da su a cikinsa, waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki sabo da shi da I’IJAZ (ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
- Ladabi tare da Allah - tsarki ya tabbatar maSa - a magana da kuma ƙudiri.
- Wajabcin yin imani da hukunci da kuma ƙaddara, da haƙuri akan cuta.
- Cutuwa ba cutarwa ba ne; mutum yana cutuwa da jin mummunan abu ko ganinsa; sai dai cewa hakan ba ya cutar da shi, kuma yana cutuwa da warin da ba'a so kamar albasa da tafarnuwa amma ba sa cutar da shi.
- Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Yana cutuwa da wasu daga ayyukan bayinSa munana, sai dai cewa Shi - Maɗaukaki - ba Ya cutuwa da hakan, kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce acikin Hadisi Ƙudsi: «Yaku bayina lallai ku baku isa ku cutar dani ballantana ku cutar daNi, kuma baku isa ku amfanar daNi ba ballatana ku amfanar daNi».
- Aibanta zamani da siffanta shi ya kasu gida uku: 1- Ya aibanta zamani akan cewa shi ne mai aikatawa; kuma cewa zamani shi ne mai jujjuya al'amura zuwa alheri ko sharri! to wannan shirka ce babba; domin ƙudircewa ne akan akwai wani mahalicci tare da Allah, kuma domin hakan danganta samar da halittu ne zuwa ga wanin Allah. 2- Ya aibata zamani badan ƙudirce cewa shi ne mai aikatawa ba, kai yana ƙudirce cewa Allah Shi ne Mai yin aiki sai dai yana aibata shi ne domin cewa shi ne mahallin wannan abun abin ƙi a wurinsa; to wannan haramun ne. 3- Ya nufi alheri tsantsa ba tare da zargi ba; to wannan ya halatta, kuma daga gare shi akwai fadin (Annabi) Lud - aminci ya tabbata agare shi -: {Kuma ya ce wannan rana ce mai tsananin wahala}.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن الله تعالى يقول في الحديث القدسي: يؤذيني ويتنقصني الإنسان الذي يسب ويذم الزمان عند نزول المصائب والمكاره؛ لأنه سبحانه هو المدبر وحده والمصرف لما يحدث؛ فالسب للزمان سب لله عز وجل، والزمان إنما هو خلْقٌ مسخّر، تجري فيه الحوادث بأمر الله تعالى.
- هذا الحديث مما يرويه النبي صلى الله عليه وسلم عن ربه، ويسمى بالحديث القدسي أو الإلهي، وهو الذي لفظه ومعناه من الله، غير أنه ليست فيه خصائص القرآن التي امتاز بها عما سواه، مِن التَّعَبُّد بتلاوته والطهارة له والتَّحَدِّي والإعجاز وغير ذلك.
- التأدب مع الله سبحانه في القول والاعتقاد.
- وجوب الإيمان بالقضاء والقدر، والصبر على الأذى.
- الأذى غير الضرر؛ فالإنسان يتأذى بسماع القبيح أو مشاهدته؛ ولكنه لا يتضرر بذلك، وأيضًا يتأذى بالرائحة الكريهة كالبصل والثوم ولا يتضرر بذلك.
- الله سبحانه وتعالى يتأذى ببعض أفعال عباده السيئة، ولكنه جل وعلا لا يتضرر بذلك، كما قال تعالى في الحديث القدسي: «يا عبادي إنكم لن تبلغوا ضري فتضروني، ولن تبلغوا نفعي فتنفعوني».
- سب الدهر ووصفه ينقسم إلى ثلاثة أقسام: 1- أن يسب الدهر على أنه هو الفاعل؛ وأن الدهر هو الذي يقلب الأمور إلى الخير والشر! فهذا شرك أكبر؛ لأنه اعتقد أن مع الله خالقًا، ولأنه نسب إيجاد الحوادث إلى غير الله، 2- أن يسب الدهر لا لاعتقاده أنه هو الفاعل؛ بل يعتقد أن الله هو الفاعل لكن يسبه لأنه محل لهذا الأمر المكروه عنده؛ فهذا محرم، 3- أن يقصد الخبر المحض دون اللوم؛ فهذا جائز، ومنه قول لوط عليه الصلاة والسلام: {وَقَالَ هَذَا يَوْمٌ عَصِيبٌ}.