Hadisai

Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرٍو رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: رَجَعْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ مَكَّةَ إِلَى الْمَدِينَةِ حَتَّى إِذَا كُنَّا بِمَاءٍ بِالطَّرِيقِ تَعَجَّلَ قَوْمٌ عِنْدَ الْعَصْرِ، فَتَوَضَّؤُوا وَهُمْ عِجَالٌ، فَانْتَهَيْنَا إِلَيْهِمْ وَأَعْقَابُهُمْ تَلُوحُ لَمْ يَمَسَّهَا الْمَاءُ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَيْلٌ لِلْأَعْقَابِ مِنَ النَّارِ أَسْبِغُوا الْوُضُوءَ».

Fassara

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun dawo tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Makka zuwa Madina har sai da muka kasance a wani ruwa a hanya, sai wasu mutane suka yi gaggawar (sallar) La'asar, sai suka yi alwala alhali suna gaggawa, sai muka kai gare su alhali karshen kafafuwanusu suna haske (lam’a) ruwa bai tabasu ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tafiya daga Makka zuwa Madina a tare da shi akwai sahabbansa, sai suka samu ruwa a hanyarsu, sai wasu daga sahabbai suka yi gaggawar alwala dan sallar La'asar har karshen kafafuwansu suka dinga bayyana ga mai kallo saboda bushewarsu daga ruwa, sai Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Azaba da halaka a cikin Wuta sun tabbata ga masu takaitawa a wanke karshen kafa a lokacin alwala, kuma ya umarcesu da sukai matuka a cikin cika alwala.

Fa'idoji

  • Wajabcin wanke kafafuwa a alwala; domin da shafa ya halatta da wanda ya bar wanke karshen kafa ba'a yi masa narko da wuta ba.
  • Wajabcin game dukkan gabban da ake wankewa da wankewa da ruwa, kuma wanda ya bar wani sashi karami daga abinda ya wajaba a wanke shi da gangan da kuma sakaci to sallarsa ba ta inganta ba.
  • Muhimmancin ilimantar da jahili da kuma shiryar da shi.
  • Malami ya yi inkarin abinda yake gani na tozartar da farillai da sunnoni ta hanyar da ta dace.
  • Muhammad Ishak al-Dahlawi ya ce: Cika (alwala) nau'i uku ne: Farilla shi ne game gaba da (ruwa) sau ɗaya, da sunna shi ne wankewa sau uku, da kuma mustahabbi shi ne tsawaitawa tare da wankewa sau uku.
Sharhi: العربية

سافَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم من مكةَ إلى المدينةِ ومعه أصحابه، وفي طريقهم وَجَدوا ماءً، فأسرع بالوضوء لصلاة العصر بعضُ الصحابة حتى إنّ مؤخَّرَ أقدامِهم يظهر للناظِر يَبُوستُها من الماء، فقال النبي صلى الله عليه وسلم: عَذابٌ وهلاكٌ في النار للمقصِّرين في غسل مؤخَّرِ القدمِ حين الوضوء، وأمرهم أن يُبالِغوا في إكمال الوضوء.

  • وجوب غسل الرجلين في الوضوء؛ لأنه لو جاز المسح لما توعّد بالنار مَن ترك غسل العقب.
  • وجوب تعميم الأعضاء المغسولة بالغسل، وأن من ترك جزءًا يسيرًا مما يجب تطهيره عمدًا وتساهلًا لا تصح صلاته.
  • أهمية تعليم الجاهل وإرشاده.
  • العالم ينكر ما يراه من تضييع الفرائض والسنن بالأسلوب المناسب.
  • قال محمد إسحاق الدهلوي: الإسباغ على ثلاثة أنواع: فرض وهو استيعاب المحل مرة، وسنة وهو الغسل ثلاثًا، ومستحب وهو الإطالة مع التثليث.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari