Hadisai

Dukkan ayyuka basa yi yiwuwa sai da niyyoyi, kuma kowanne mutum yana da ladan abin da ya niyyata ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce ne[Limaman Malaman Hadisi guda biyu ne suka rawaito shi, Abu Abdullahi Muhammad bn Isma'il bn Ibrahim bn al-Mughirah bn Bardizbah al-Bukhari, da Abul Husain Muslim bn al-Hajjaj bn Muslim al-Kushairi an-Naisaburi, a cikin Sahihansu guda biyu, waɗanda su ne m

Rubutun Larabci

عَنْ أَمِيرِ المُؤْمِنِينَ أَبِي حَفْصٍ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لِكُلِّ امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ لِدُنْيَا يُصِيبُهَا أَوْ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إلَى مَا هَاجَرَ إلَيْهِ».

Fassara

Daga sarkin muminai baban Hafs Umar ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Dukkan ayyuka basa yi yiwuwa sai da niyyoyi, kuma kowanne mutum yana da ladan abin da ya niyyata ne wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da ManzonSa to hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa, wanda hijirarsa ta kasance dan duniya da zai sameta ko wata mace da zai aureta to hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gare shi».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a cikin dukkanin ayyuka na ibadu da mu'amaloli, wanda ya yi nufin wani abin amfani da aikinsa ba zai samu komai ba sai wannan abin amfanin, kuma babu sakamako gareshi, wanda yayi nufin neman kusanci da aikinsa zuwa ga Allah - madaukakin sarki zai samu sakamako da lada daga aikinsa ko da aikin ya kasance na al'ada ne, kamar ci da sha. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don bayanin tasirin niyya a ayyuka tare da daidaituwarsu a sura ta zahiri, sai ya bayyana cewa wanda ya yi nufin neman yardar Ubangigjinsa da hijirarsa, to, hijirarsa hijira ce ta shari'a abar karɓa za a yi masa sakayya a kanta don gaskiyar niyyarsa, wanda ya yi nufin wani abin amfani na duniya na dukiya, ko kasuwanci, ko mata da hijirarsa ba zai samu komai daga hijirarsa ba sai wancan abin amfanin da ya yi niyyarsu, kuma ba zai samu lada da sakamako ba.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa a kan ikhlasi, domin Allah ba Ya karɓar aiki sai abin da aka nufi zatinsa da shi.
  • Ayyukan da ake neman kusancin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da su idan mukallafi ya aikata su a kan tafarkin al'ada, to, ba shi da wani lada a kansu, har sai ya yi nufin neman kusancin Allah da su.
  • Niyya da ita ne ake banbancewa tsakaknin ibadu sashinsu da sashi, kuma (da itane ake banbancewa tsakanin) ibadu da al'adu.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ كل الأعمال معتبرة بالنية، وهذا الحكم عام في جميع الأعمال من العبادات والمعاملات، فمن قصد بعمله منفعةً لم يَنَلْ إلا تلك المنفعة ولا ثواب له، ومن قصد بعمله التقرب إلى الله تعالى نال من عمله المثوبة والأجر ولو كان عملًا عاديًّا، كالأكل والشرب. ثم ضرب صلى الله عليه وسلم مثلًا لبيان تأثير النية في الأعمال مع تساويهما في الصورة الظاهرة، فبَيَّن أنَّ من قصد بهجرته وترك وطنه ابتغاء مرضات ربه، فهجرته هجرة شرعية مقبولة يثاب عليها لصدق نيته، ومن قصد بهجرته منفعةً دنيوية، من مال، أو جاه، أو تجارة، أو زوجة، فلا ينال من هجرته إلا تلك المنفعة التي نواها، ولا نصيب له من الأجر والثواب.

  • الحث على الإخلاص، فإن الله لا يقبل من العمل إلا ما ابتُغي به وجهه.
  • الأعمال التي يُتَقَرَّبُ بها إلى الله عز وجل إذا فعلها المكلف على سبيل العادة ليس له ثواب عليها، حتى يقصِدَ بها التقرب إلى الله.
  • النية يفرق بها بين العبادات بعضها عن بعض وأيضًا العبادات عن العادات.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari