Hadisai

Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na horeku da sunnata da kuma sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي نَجِيحٍ العِرْبَاضِ بْنِ سَارِيَةَ رضي الله عنه قَالَ: وَعَظَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَوْعِظَةً وَجِلَتْ مِنْهَا القُلُوبُ، وَذَرَفَتْ مِنْهَا العُيُونُ، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ! كَأَنَّهَا مَوْعِظَةُ مُوَدِّعٍ؛ فَأَوْصِنَا، قَالَ: «أُوصِيكُمْ بِتَقْوَى اللَّهِ، وَالسَّمْعِ وَالطَّاعَةِ، وَإِنْ تَأَمَّرَ عَلَيْكُمْ عَبْدٌ، فَإِنَّهُ مَنْ يَعِشْ مِنْكُمْ بَعْدِي فَسَيَرَى اخْتِلَافًا كَثِيرًا، فَعَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ الخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ المَهْدِيينَ، عَضُّوا عَلَيْهَا بِالنَّوَاجِذِ، وَإِيَّاكُمْ وَمُحْدَثَاتِ الأُمُورِ؛ فَإِنَّ كُلَّ بِدْعَةٍ ضَلَالَةٌ».

Fassara

Daga Abu Najih Irbad ibn Sariyah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana wa’azi, wa’azin da zukata suka firgita daga gare shi, kuma idanuwa suka zub da hawaye daga gare shi, muka ce: Ya Manzon Allah! kamar wa’azin mai bankwana, ka yi mana wasiyya, sai ya ce: «Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na horeku da sunnata da kuma sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa Ku riƙeta da turaman haƙoranku, na haneku daga fararrun al'amura; domin dukkanin bidi'a ɓata ce».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa wa'azi wa'azi isasshe zukata sun ji tsoro daga gare shi, kuma idanuwa sun zubar da hawaye daga gare shi, Sai suka ce : Ya Manzon Allah ! kai ka ce wannan wa'azin bankwana ne, saboda abinda suka gani ya kai matukarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wa'azi, sai suka nemi wata wasiyyar dan su yi riko da ita a bayansa, Ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah - Mai girma da daukaka -, hakan da aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, da ji da bi, wato: Ga shugabanni, koda bawa ne ya shugabanceku ko ya yi rinjaye a kanku, wato ya zama mafi kaskantar halitta sarki akanku kada ku hanu daga hakan, ku bi shi dan tsoron tada fitintinu, domin shi wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Sannan ya bayyana musu mafita daga wannan sabanin, hakan dayin riko da sunnarsa da sunnar Halifofi shiryayyu a bayansa, Abu bakar Al-Siddik, da Umar Dan Al-khaddab, da Usman Dan Affan, da Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda su baki daya -, da riketa da turamen hakora wato - turamen hakora na karshe -: Yana nufi da hakan kokari a lazimtar sunna da yin riko da ita, ya kuma gargadesu daga fararrun al'amura kirkirarru a Addini, domin cewa kowacce bidi'a bata ce.

Fa'idoji

  • Muhimmancin riko da sunna da kuma binta.
  • Kula da wa'azuzzuka da kuma tausasa zukata.
  • Umarni da bin Halifofi masu shiryarwa su hudu a bayansa, su ne Abubakar da Umar da Usman da Aliyu - Allah Ya yarda da su -.
  • Hani daga kirikira a Addini, kuma cewa kowacce bidi'a bata ce.
  • Ji da bi ga wanda ya jibinci al'amarin muminai in ba sabo ba ne.
  • Muhimmancin tsoron Allah - Mai girma da daukaka - a dukkanin lokuta da halaye.
  • Sabani mai afkuwane a cikin wannan al'ummar, a yayin faruwarsa to yana wajaba komawa zuwa sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Halifofinsa masu shiryarwa.
Sharhi: العربية

وَعَظَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أصحابَه مَوعظةً بَلِيْغَةً خافتْ منها القلوبُ ودَمَعتْ منها العيونُ، فقالوا: يا رسول الله كأنها مَوعظةُ مُودِّعٍ لِمَا رأوا مِن مبالغتِه صلى الله عليه وسلم في الموعظة، فطلبوا وصيةً ليتمسكوا بها مِن بعده، قال: أوصيكم بتقوى الله عز وجل، وذلك بفعل الواجبات وترك المحرمات، والسمع والطاعة، أي: للأمراء، وإنْ تَأَمَّر عليكم عَبْدٌ أو استولى عليكم، أي صار أدنى الخَلْقِ أميرًا عليكم فلا تَسْتَنْكِفُوا عن ذلك وأطيعوه، مخافةَ إثارةِ الفتن، فإنه مَن يعِش منكم فسيرى اختلافًا كثيرًا، ثم بَيَّنَ لهم المَخْرَجَ مِن هذا الاختلاف، وذلك بالتمسُّك بِسُنَّتِهِ وسُنّةِ الخلفاء الراشدين المهديين مِن بعده، أبي بكر الصديق، وعمر بن الخطاب، وعثمان بن عفان، وعلي بن أبي طالب رضي الله عنهم أجمعين، والعَضُّ عليها بالنواجذ أي –الأضراس الأخيرة-: يعني بذلك الجِدُّ في لزوم السنة والتمسك بها، وحَذَّرَهم من الأمور المُحدَثة المُبْتَدَعة في الدِّين، فإنِّ كلَّ بدعةٍ ضلالةٌ.

  • أهمية التَّمَسُّكِ بالسُّنّة واتباعها.
  • العناية بالمواعظ وترقيق القلوب.
  • الأمر باتباع الخُلَفاء الراشدين المهديين الأربعة مِن بعده، وهم أبو بكر وعمر وعثمان وعلي رضي الله عنهم.
  • النهيُ عن الابتداع في الدِّين، وأنّ كل البدع ضلالة.
  • السمع والطاعة لمَن تولَّى أمر المؤمنين في غير معصية.
  • أهمية تقوى الله عز وجل في كل الأوقات والأحوال.
  • الاختلاف واقع في هذه الأمة، وعند حدوثِهِ يلزم الرجوعُ إلى سُنّة رسول الله صلى الله عليه وسلم والخلفاء الراشدين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari