Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ النَّوَّاسِ بْنِ سِمْعَانَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «البِرُّ: حُسْنُ الخُلُقِ، وَالإِثْمُ مَا حَاكَ فِي صَدْرِكَ، وَكَرِهْتَ أَنْ يَطَّلِعَ عَلَيْهِ النَّاسُ». وَعَنْ وَابِصَةَ بْنِ مَعْبَدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: أَتَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «جِئْتَ تَسْأَلُ عَنِ البِرِّ وَالإِثْمِ»، قُلْتُ: نَعَمْ، قَالَ: «اسْتَفْتِ قَلْبَكَ، البِرُّ: مَا اطْمَأَنَّتْ إلَيْهِ النَّفْسُ، وَاطْمَأَنَّ إلَيْهِ القَلْبُ، وَالإِثْمُ: مَا حَاكَ فِي نَفْسِكَ وَتَرَدَّدَ فِي الصَّدْرِ، وَإِنْ أَفْتَاكَ النَّاسُ وَأَفْتَوْكَ».
Fassara
Daga Nawwas Ibnu Sam'an al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «al-Birr shi ne: Kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abin da ya sosu a cikin zuciya, kuma ka ƙi mutane su tsinkaya a kansa». Daga Wabisa ibnu Ma'abad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Kazo ne kana tambaya game da al-birr da zunubi?», na ce: Eh, ya ce: «Ka tambayi zuciyarka, al-birr: Abin da ranka ya natsu zuwa gare shi, kuma zuciya ta nutsu gare shi, zunubi kuma: Abin da ya sosu a cikin zuciyarka kuma ya kaikawo a cikin ƙirji, ko da mutane sun baka fatawa kuma sun baka fatawa».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da al-birr da kuma zunubi, sai ya ce: Lallai mafi girman ɗabi'un al-birr su ne kyawawan ɗabi'u tare da Allah ta hanyar jin tsoron Allah, haka tare da halitta ta hanyar jure cuta, da ƙarancin fushi, da shimfiɗar fuska, daddaɗan zance, da sadar da zumunci, da biyayya da tausasawa da kuɓutarwa, da kyakkyawar mu'amala da abokantaka, kuma cewa al-birr shi ne abin da zuciya da rai suka nutsu gare shi. Amma zunubi to abin da ya kaikawo a cikin zuciya na abubuwa masu rikitarwa kuma ya kaikawo ba tare da ƙirji ya samu natsuwa daga gareshi ba, kuma kokwanto ya faru daga gare shi a cikin zuciya, da jin tsoron kasancewarsa zunubi ne, kuma baka son ka bayyanar da shi dan kasancewarsa mummuna a idanuwa da mutanen kirki da cikakkun mutane, hakan domin rai a ɗabi'arsa yana son ganin mutane akan alherinsa, idan rai ya ƙi tsinkaya akan wasu daga cikin ayyukansa to shi zunubi ne babu alheri a cikinsa; ko da mutane sun baka fatawa to kada ka ɗauki fatawarsu muddin dai alamar shubha tana kaikawo a cikin ranka, domin fatawa bata kawar da shubha muddin dai shubhar ingantacciya ce, kuma mai bada fatawa yana bada fatawa ba tare da ilimi ba; amma idan fatawar gini ce akan wani dalili na shari'a to wajibi akan mai neman fatawa shi ne ya koma zuwa gare ta, ko da ƙirjinsa bai budeba gareta ba.
Fa'idoji
- Kwaɗaitarwa akan kyawawan ɗabi'u; domin kyawawan ɗabi'u suna daga mafi girman ɗabi'un aikin alheri.
- Gaskiya da ƙarya al'amarinsu ba ya rikitarwa ga mumini, kai yana sanin gaskiya da hasken da ke cikin zuciyarsa, kuma yana gujewa ƙarya sai ya yi musunta.
- Daga alamomin zunubi kaikawon zuciya, da ƙin tsinkayar mutane a kansa.
- Sindi ya ce: Wannan a abubuwa masu rikitarwa ne waɗanda mutane ba sa sanin hakikanin ɗayan ɓangarori biyun daga cikinsu; inba haka ba abin umarni da shi acikin shari'a ba tare da bayyanar dalili a cikinsa ba akan saɓanin hakan daga aikin alheri, abin hanawa daga gare shi kamar hakan, babu buƙatuwa a cikinsu zuwa neman bada fatawar zuciya da kuma nutsuwarta.
- Wandanda akewa magana a cikin hadisin (su ne) ma'abota nagartacciyar ɗabi'a, ba ma'abota karkatattun zukata ba waɗanda ba sa sanin aikin alheri kuma ba sa ƙin abin ƙi sai dai abinda aka cakuɗa daga son ransu kawai.
- Ɗibi ya ce: An ce an fassara al-Birr a cikin hadisin da ma'anoni da yawa, ya fassara shi a wani wuri da abinda ransa ya nutsu kuma zuciyarsa ta nutsu da shi, kuma ya fassara shi a wani wurin daban da imani, a wani wurin kuma da abinda zai kusantoka zuwa ga Allah, a nan da kyakkyawar ɗabi'a, an fassara kyakkyawar ɗabi'a: Da jurewa cuta da ƙarancin fushi da shinfiɗar fuska da daddaɗan zance, dukkansu masu kusantar junane a ma'ana.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم عن البر والإثم، فقال: إن أعظم خصال البر حسن الخُلُق مع الله بالتقوى، ومع الخَلْق باحتمال الأذى، وقلة الغضب، وبسط الوجه، وطيب الكلام، والصلة والطاعة واللطف والمبرة وحسن العشرة والصحبة. وأن البر ما سكن إليه القلب والنفس. وأما الإثم فما تحرك في النفس من المشتبهات وتردد دون أن ينشرح الصدر له، وحصل في القلب منه الشك، والخوف من كونه ذنبًا، ولم تُرد أن تظهره لكونه قبيحًا لأعيان وأماثل الناس وكُمَّلِهم، وذلك لأن النفس بطبعها تحب اطلاع الناس على خيرها، فإذا كَرِهَت الاطلاع على بعض أفعالها فهو إثم لا خير فيه؛ وإن أفتاك الناس فلا تأخذ بفتواهم ما دامت علامة الشبهة تتردد في نفسك فإن الفتوى لا تزيل الشبهة ما دامت الشبهة صحيحة وكان المفتي يفتي بغير علم؛ أما إذا كانت الفتوى بناء على دليل شرعي فالواجب على المستفتي الرُّجوعُ إليه، وإنْ لم ينشرح له صدرُه.
- الحثُّ على مكارم الأخلاق؛ لأنّ حسن الخلق من أعظم خصال البر.
- الحق والباطل لا يلتبس أمرُهما على المؤمن، بل يعرف الحق بالنور الذي في قلبه، وينفر عن الباطل فينكره.
- من علامات الإثم قلق القلب واضطرابه، وكراهة اطلاع الناس عليه.
- قال السندي: هذا في المشتبهات من الأمور التي لا يعلم الناس فيها بتعيين أحد الطرفين؛ وإلا فالمأمور به في الشرع من غير ظهور دليل فيه على خلاف ذلك من البر، والمنهي عنه كذلك من الإثم، ولا حاجة فيهما إلى استفتاء القلب وطمأنينته.
- المخاطَب في الحديث أصحاب الفطرة السليمة، لا أصحاب القلوب المنكوسة التي لا تعرف معروفًا ولا تنكر منكرًا إلا ما أُشرِبتْ من هواها.
- قال الطيبي: قيل فُسِّرَ البر في الحديث بمعان شتى، ففسَّره في موضع بما اطمأنت إليه النفس واطمأن إليه القلب، وفسره في موضع بالإيمان، وفي موضع بما يقربك إلى الله، وهنا بحسن الخلق، وفسر حسن الخلق: باحتمال الأذى وقلة الغضب وبسط الوجه وطيب الكلام، وكلها متقاربة في المعنى.