Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: لعن رسول الله صلى الله عليه وسلم الرجل يلبس لِبْسَةَ المرأة، والمرأة تلبس لِبْسَةَ الرجل.
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah ga dukkan namijin da ya yi kama da mace a cikin tufafin da suka keɓanci mata; daidai ne a cikin kama ne ko launi ko kaifiyya ko hanyar sanyawa da ado ko wanin haka. Ko mace ta yi kama da kayan da suka keɓanci maza kamar haka, kuma shi laifi ne babba daga manyan laifuka.
Fa'idoji
- AlShaukani ya ce: Haramcin kamanceceniyar mata da maza da maza da mata; domin cewa tsinuwa ba ta kasancewa sai akan aikata haram.
- Ibnu Usaimin ya ce: Abinda ya kasance abin tarayya ne tsakaninsu misalin sashin fanilolin da maza da mata suke sanyawa to cewa wannan babu laifi da shi, wato babu laifi maza da mata su ɗaura su; domin cewa shi sun yi tarayya ne.
Sharhi: العربية
دَعَا النبيُّ صلى الله عليه وسلم بالطَّرْدِ والإبعاد من رحمة الله لكلِّ رجلٍ يتشبَّه بالمرأة في الملابس الخاصة بالنساء؛ سواء في الهيئة أو اللون أو الكيفية أو طريقة اللبس والزينة أو غير ذلك، أو أن تتشبَّهَ المرأةُ باللبس الخاص بالرجال كذلك، وهو كبيرة من كبائر الذنوب.
- قال الشوكاني: تحريم تشبه النساء بالرجال والرجال بالنساء؛ لأن اللعن لا يكون إلا على فعل محرم.
- قال ابن عثيمين: ما كان مشتركًا بينهما مثل بعض الفنائل التي يلبسها الرجل والنساء فإنه لا بأس به، أي لا بأس أن يلبسَه الرجال والنساء؛ لأنه مشترك.