Hadisai

Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيَّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ -وَكَانَ غَزَا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ثِنْتَيْ عَشْرَةَ غَزْوَةً- قَالَ: سَمِعْتُ أَرْبَعًا مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَعْجَبْنَنِي، قَالَ: «لاَ تُسَافِرِ المَرْأَةُ مَسِيرَةَ يَوْمَيْنِ إِلَّا وَمَعَهَا زَوْجُهَا أَوْ ذُو مَحْرَمٍ، وَلاَ صَوْمَ فِي يَوْمَيْنِ: الفِطْرِ وَالأَضْحَى، وَلاَ صَلاَةَ بَعْدَ الصُّبْحِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ، وَلاَ بَعْدَ العَصْرِ حَتَّى تَغْرُبَ، وَلاَ تُشَدُّ الرِّحَالُ إِلَّا إِلَى ثَلاَثَةِ مَسَاجِدَ: مَسْجِدِ الحَرَامِ، وَمَسْجِدِ الأَقْصَى، وَمَسْجِدِي هَذَا».

Fassara

Daga Abu sa'id AlKhudr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance ya yi yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yaƙi goma sha biyu - ya ce: Na ji abubuwa hudu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka ƙayatar dani, ya ce: "Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta, Babu azumi a ranaku biyu: Karamar sallah da babbar sallah, kuma babu sallah bayan asuba har sai rana ta bullo, kuma babu bayan la'asar har sai ta fadi, kuma ba'a daure sirdi (nikar gari domin tafiya) sai a masallatai uku: Masallaci mai alfarma, da masallacin Kudus, da masallacina wannan".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana abubuwa hudu: Na farkonsu: Hana mace daga tafiyar kwana biyu ba tare da mijinta ba ko daya daga muharramanta ba, shi ne wanda ta haramta agare shi haramci na har'bada daga 'yan uwa, kamar Da, da uba, da Dan dan uwa da dan 'yar uwa, da baffa da kawu, da makamancin hakan. Na biyunsu: Hani daga azimin ranar ƙaramar sallah da ranar babbar sallah, duk daya ne musulmi ya azimce su ne akan bakance (alwashi) ko nafila, ko kuma kaffara. Na ukunsu: Hani daga sallar nafila bayan sallar la'asar har sai rana ta fadi, da bayan bullowar alfijir har sai rana ta bullo. Na hudunsu: Hani daga tafiya zuwa wani wuri daga wurare da ƙudirce falalarsu da ƙudirce ninkin kyawawan lada a cikinsu, in banda wadannan masallatan uku, to ba'a daure sirdi ga wasunsu dan yin sallah a cikinsu, domin lada ba'a ninkashi sai a wadannan masallatan uku: Masallaci mai alfarma (Dake Makka), da masallacin Annabi (Dake Madina), da masallacin Kudus (Dake Falasdin).

Fa'idoji

  • Rashin halaccin tafiyar mace ba tare da muharrami ba.
  • Mace ba muharrama ba ce ga mace a tafiya; Saboda fadinsa: "Mijinta ko muharraminta".
  • Dukkan abinda ake kira tafiya to mace an hanata ta yi ba tare da miji ko muharrami ba, wannan hadisin ya kasance ne gwargwadan halin mai tambaya da wurinsa.
  • Muharamin mace shi ne mijinta ko wanda ya haramta ta aure shi har abada, saboda kusanci kamar uba da Da da baffa da kawu. Ko shayarwa kamar uba na shayarwa da baffa na shayarwa, ko surukuta kamar baban miji, kuma ya zama musulmi baligi mai hankali amintacce, domin abin nufi daga muaharrami kare mace da tsareta da tsayuwa da sha'aninta.
  • Kulawar shari'ar Musulunci da mace, da kareta da tsareta.
  • Rashin ingancin sallar nafila kowacce bayan sallar Asuba da la'asar, an toge daga hakan rama farillan da suka wuce, da masu sabubba, kamar gaisuwar masallaci da makamancin hakan.
  • Sallah ta haramta bayan bullowar rana kai tsaye, domin babu makawa sai ta dago gwargwadan goron mashi, da abinda ya yi kusa na mintina goma zuwa sha biyar a kusance.
  • Lokacin la'asar yana mikewa zuwa faduwar rana.
  • A cikinsa akwai halaccin daure sirdi (domin tafiya) zuwa masallatai uku.
  • Falalar masallatai uku da fifikonsu akan wasunsu.
  • Rashin halaccin tafiya dan ziyartar ƙaburbura koda ya kasance ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ne, amma ziyararsa ta halatta ga wanda yake a Madina, ko ya zo Madina dan wata buƙatar da aka shara'anta ko aka halatta.
Sharhi: العربية

نَهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم عَن أربعة أمور: أولها: منع المرأة من السفر مَسيرة يومين بدون زوجِها أو أحدٍ محارمِها وهو مَن حَرُمتْ عليه تحريمًا مؤبدًا مِن الأقارب، كالابن والأب، وابن الأخ وابن الأخت، والعم والخال، ونحو ذلك. ثانيها: النهي عن صوم يوم عيد الفطر ويوم عيد الأضحى، وسواء صامهما المسلم عن نَذْر، أو تطوُّع، أو كفارة. ثالثها: النهي عن صلاة التطوع بعد صلاة العصر حتى تغرب الشمس، وبعد طلوع الصبح حتى تطلع الشمس. رابعها: النهي عن السفر إلى بُقْعَة من البِقاع واعتقاد فضلها واعتقاد مضاعفة الحسنات فيها غير هذه المساجد الثلاثة فلا تُشد الرحال لغيرها لأجل الصلاة فيها، فإنَّ الأجر لا يُضاعف إلا في هذه المساجد الثلاثة، المسجد الحرام، والمسجد النبوي، والمسجد الأقصى.

  • عَدم جواز سَفر المرأة بلا مَحْرم.
  • المرأة ليست محرمًا للمرأة في السَّفر؛ لقوله: "زوجُها أو ذو محرم".
  • كلُّ ما يُسمى سفرًا فإن المرأة تُنهى عنه بغير زوج أو مَحرم، وهذا الحديث كان بحسب حال السائل وموطنه.
  • مَحْرَم المرأة هو زوجها أو من يحرم عليها الزواج منه بالتأبيد بسببِ قرابةٍ كالأب والابن والعم والخال، أو رضاع كالأب من الرضاع والعم من الرضاع، أو مصاهرة كأبي الزوج، ويكون مسلمًا بالغًا عاقلًا ثقة مأمونًا، فإنَّ المقصود من المحرم حمايةُ المرأة وصيانتُها والقيام بشأنها.
  • اعتناء الشريعة الإسلامية بالمرأة، وحمايتها وصَونها.
  • عدم صحة صلاة التطوع المُطْلق بعد صلاة الفجر والعصر، ويُستثنى مِن ذلك قضاء الفرائض الفوائت، وذوات الأسباب كتحيَّة المسجد ونحو ذلك.
  • تَحْرُم الصلاة بعد طلوع الشمس مباشرة، بل لابد من ارتفاعها قَدْرَ رمحٍ، بما يُقارب عشرَ دقائق إلى ربع ساعة تقريبًا.
  • وقت العصر يَمتدُّ إلى غروب الشمس.
  • فيه جواز شَد الرِّحال إلى المساجد الثلاثة.
  • فضل المساجد الثلاثة ومَزِيَّتُها على غيرها.
  • عدم جواز السفر لزيارة القبور ولو كان قَبر النبي صلى الله عليه وسلم، وتجوز زيارته لمن كان في المدينة، أو أتى إليها لغرضٍ مشروعٍ أو جائز.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari