Hadisai

Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a kasuwa, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana yin afuwa kuma yana kau da kai

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neTirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن أَبي عَبْدِ اللهِ الْجَدَلِيِّ قَالَ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها عَنْ خُلُقِ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم فَقَالَتْ: لَمْ يَكُنْ فَاحِشًا وَلَا مُتَفَحِّشًا وَلَا صَخَّابًا فِي الْأَسْوَاقِ، وَلَا يَجْزِي بِالسَّيِّئَةِ السَّيِّئَةَ وَلَكِنْ يَعْفُو وَيَصْفَحُ.

Fassara

Daga Abu Abdullahi al-Jadali ya ce: Na tambayi A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a kasuwa, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana yin afuwa kuma yana kau da kai.

Sharhi

An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Alfasha da munanan maganganu ko ayyuka ba su zama daga ɗabi'unsa ba, kuma ba ya ɗorawa kansa alfasha, kuma ba ya yi da gangan, kuma ba ya ihu yana ɗaga muryarsa a cikin kasuwanni, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana sakayya da kyakkyawa, kuma yana yin afuwa a baɗini, kuma yana kau da kai yana kawar dakai a zahiri.

Fa'idoji

  • Bayanin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yake a kansa na manyan ɗabi'u, da nisanta daga ɗabi'u ababen zargi.
  • Kwaɗaitarwa akan aikata kyawawan ɗabi'u da kuma nisantar munanan ɗabi'u.
  • Zargin yin magana da munananawa a magana da kuma mummunan zance.
  • Zargin ɗaga murya ga mutane dayi musu ihu.
  • Kwaɗaitarwa akan rama mummuna da kyakkyawan abu da kuma yin afuwa da kau da kai.
Sharhi: العربية

سُئلت أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها عن خُلق النبي صلى الله عليه وسلم فقالت: لم يكن في طبعه الفحش والقبح بأقواله وأفعاله، ولا يتكلف الفحش ولا يتعمده، ولا صيّاحًا يرفع صوته في الأسواق، ولا يجزي بالسيئة السيئة؛ ولكن يجزي بالحسنة، ويعفو في الباطن، ويصفح ويعرض عنه في الظاهر.

  • بيان ما كان عليه النبي صلى الله عليه وسلم من الخلق الرفيع والبعد عن الأخلاق الذميمة.
  • الحث على فعل الأخلاق الحسنة والابتعاد عن الأخلاق السيئة.
  • ذم التكلم بالبذيء من القول والكلام القبيح.
  • ذم رفع الصوت على الناس والصياح عليهم.
  • الحث على مقابلة الإساءة بالحسنة والعفو والمسامحة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari