Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما: سَأَلَ رَجُلٌ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ عَلَى المِنْبَرِ، مَا تَرَى فِي صَلاَةِ اللَّيْلِ، قَالَ: «مَثْنَى مَثْنَى، فَإِذَا خَشِيَ الصُّبْحَ صَلَّى وَاحِدَةً، فَأَوْتَرَتْ لَهُ مَا صَلَّى» وَإِنَّهُ كَانَ يَقُولُ: «اجْعَلُوا آخِرَ صَلاَتِكُمْ وِتْرًا» فَإِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَمَرَ بِهِ.
Fassara
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce», idan ya ji tsoron (ɓullowar) Asuba sai ya sallaci raka'a ɗaya, sai ta yi masa wutirin abin da ya sallata» kuma shi ya kasance yana cewa «Ku sanya ƙarshen sallarku ta zama witiri» domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.
Sharhi
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tattaba agare shi - a lokacin yana huɗuba akan mimbari: Ya Manzon Allah ka sanar da ni yaya zan yi sallar dare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka yi sallah ka sallame daga kowadanne raka’oi biyu, idan ka ji tsoron ɓullowar asuba to ka sallaci raka'a ɗaya sai ta yi maka wutirin abin da ka sallata, kuma cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wasicci da a sanya ƙarshen sallar dare ta zama witiri.
Fa'idoji
- Asali a cikin sallar dare shi ne ya yi sallama daga kowadanne raka’oi biyu, banda witiri.
- Cewa sallar dare ba'a ƙayyade ta da wani adadi ba; dan wawaitar da lafazin.
- Nawawi ya ce: "Sallar dare da rana raka'a biyu-biyu ce", wannan abin ɗauka akan bayanin a bin da ya fi, shi ne ya yi sallama daga kowanne raka’oi biyu, kuma daidai ne nafilfilin dare da na rana an so mai sallah ya yi sallama daga kowanne raka’oi biyu.
- Nawawi ya ce: A cikin wannan a kwai dalili akan sunna ita ce a sanya witiri a ƙarshen sallar dare, kuma lokacinsa yana fita ne da zarar alfijir ya ɓullo, shine mafi shahara a mazahabarmu, kuma da shi ne jumhur na malamai suka faɗa.
Sharhi: العربية
سأل رجل النبي صلى الله عليه وسلم وهو يخطب على المنبر: يا رسول الله علمني كيف أصلي الليل؟ فقال صلى الله عليه وسلم: تصلي وتسلم من كل ركعتين، فإذا خفت طلوع الصبح فصلِّ ركعة توتر لك ما صليت، وإنه صلى الله عليه وسلم كان يوصي بجعل آخر صلاة الليل وترًا.
- الأصل في صلاة الليل أن يسلِّم من كل ركعتين، في غير الوِتر.
- أن صلاة الليل غير مُقيدة بعَدد؛ لإطلاق اللفظ.
- قال النووي: "صلاة الليل والنهار مثنى مثنى"، هذا الحديث محمول على بيان الأفضل، وهو أن يسلم من كل ركعتين، وسواء نوافل الليل والنهار يستحب أن يسلم من كل ركعتين.
- قال النووي: فيه دليل على أن السنة جعل الوتر آخر صلاة الليل، وعلى أن وقته يخرج بطلوع الفجر، وهو المشهور من مذهبنا، وبه قال جمهور العلماء.