Hadisai

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُعْجِبُهُ التَّيَمُّنُ، فِي تَنَعُّلِهِ، وَتَرَجُّلِهِ، وَطُهُورِهِ، وَفِي شَأْنِهِ كُلِّهِ.

Fassara

Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana so kuma yana fifita cewa ya fara da dama a al'amuransa masu dacewa da girmamawa, daga cikin hakan: Ya fara da kafar dama a sanya takalminsa, kuma yana farawa da dama a taje gashin kansa da gemunsa a tajesu da shafa musu mai, a alwalarsa kuma yana gabatar da dama akan hagu daga hannaye da kafafuwa.

Fa'idoji

  • Nawawi ya ce: Wannan ka'ida ce tabbatacciya a shari'a, ita ce: cewa abinda ya kasance daga babin giramamawa da daukaka, kamar sanya tufa da wanduna da huffi da shiga masallaci da asuwaki da sanya kwalli, da yanke farce, da rage gashin baki, da taje kai shi ne yi masa kum, da cire gashin hammata, da aske kai, da sallama daga sallah, da wanke gabban alwala, da fita daga bandaki, da ci da sha, da musafaha, da sumbatar (Alhajarul Aswad) bakin dutse, da wanin hakan na abinda yake a cikin ma'anarsa anso damantawa a cikinsa. Amma abinda ya kasance kishiyarsa kamar shiga bandaki, da fita daga masallaci da face majina, da tsarki, da tube tufafi da wanduna da huffi da abinda ke kama da hakan, to an so haguntawa a cikinsa, wannan saboda girmama dama da kuma daukakarta.
  • "Damantawa yana kayatar da shi". Ya kunshi: Farawa a cikin ayyuka da hannun dama, da kafar dama, da bangaren dama, da bada abu da dama.
  • Nawawi ya ce: Ka sani cewa daga gabban alwala a kwai wadanda ba’a son damantawa a cikinsu; shi ne kunnuwa da tafuka da kundukuki kai za'a tsarkakesu ne karo daya, idan hakan ya wuyata kamar a hakkin mai dungu da makamancinsa; sai a gabatar da dama.
Sharhi: العربية

كانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم يحبُّ ويفضِّل أن يبدأ باليمين في أموره اللائقة بالتكريم، ومن ذلك: أن يبدأ بالرِّجْل اليمين في لبس نعله، ويبدأ باليمين في ترجيل شعر رأسه ولحيته وتسريحِهما ودَهنِهما، وفي وضوئه يقدِّم اليمين على اليسار من اليدين والرجلين.

  • قال النووي: هذه قاعدة مستمرة في الشرع، وهي أنَّ ما كان من باب التكريم والتشريف كلبس الثوب والسراويل والخُفِّ ودُخول المسجد والسواك والاكتحال، وتقليم الأظفار، وقص الشارب، وتَرْجِيْل الشَّعَرِ وهو مَشْطُه، ونتف الإبط، وحلق الرأس، والسلام من الصلاة، وغسل أعضاء الطهارة، والخروج من الخلاء، والأكل والشرب، والمصافحة، واستلام الحجر الأسود، وغير ذلك مما هو في معناه يستحب التيامن فيه، وأما ما كان بضده كدخول الخلاء والخروج من المسجد والامتخاط والاستنجاء وخلع الثوب والسراويل والخف وما أشبه ذلك، فيستحب التياسر فيه، وذلك كله بكرامة اليمين وشرفها.
  • "يعجبه التيمن"، يشمل: الابتداء في الأفعال باليد اليمنى، والرجل اليمنى، والجانب الأيمن، وتعاطي الشيء باليمين.
  • قال النووي: اعلم أن من أعضاء الوضوء ما لا يستحب فيه التيامن؛ وهو الأذنان والكفان والخدان بل يُطَهَّران دفعة واحدة، فإن تعذَّر ذلك كما في حق الأقطع ونحوه؛ قَدَّمَ اليمين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari