Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neTirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُكْثِرُ أَنْ يَقُولَ: «يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، آمَنَّا بِكَ وَبِمَا جِئْتَ بِهِ فَهَلْ تَخَافُ عَلَيْنَا؟ قَالَ: «نَعَمْ، إِنَّ القُلُوبَ بَيْنَ أُصْبُعَيْنِ مِنْ أَصَابِعِ اللهِ يُقَلِّبُهَا كَيْفَ يَشَاءُ».

Fassara

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa" sai na ce: Ya Manzon Allah, mun yi imani da kai da kuma abinda ka zo da shi, shin kana jin tsoro akanmu ne? ya ce: "Eh, lallai zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana jujjuyasu yadda Ya ga dama".

Sharhi

Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance rokon Allah ne tabbata akan addini da biyayya, da nisanta daga karkata da kuma bata, Sai Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamakin yawaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wannan addu'ar, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin cewa zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana juyasu yadda Ya ga dama, Zuciya ita ce gurin imani da kafirci, hakika an anbaci zuciya (Kalbu) saboda yawan jujjuawarta; ita ce mafi tsananin jujjuyawa daga tukunya idan ta tafarfasa, wanda Allah Ya so Zai tsaida zuciyarsa akan shiriya, ya tabbatar da shi akan addini, wanda Allah Ya ga dama kuma Zai juyar da zuciyarsa daga shiriya zuwa karkata da bata.

Fa'idoji

  • Kankan da kan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa da kankar dakai gareShi, da nunawa al'umma rokon hakan.
  • Muhimmancin tsayuwa akan gaskiya da tabbata akan addini, kuma izina da karshe ne.
  • Bawa ba ya wadatuwa daga Allah Ya tabbatarwa shi akan musulunci koda kiftawar ido.
  • Kwadaitarwa akan yawaita wannan addu'ar dan koyi da Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -.
  • Tabbata akan musulunci shi ne ni'ima mafi girma wacce yake kamata ga bawa ya yi kokari gareta kuma ya godewa Ubangijinsa akanta.
Sharhi: العربية

كانَ أكثرُ دعاء النبي صلى الله عليه وسلم سؤال الله الثّبات على الدين والطاعة، والبعد من الزيغ والضلال، فتعجَّب أنس بن مالك رضي الله عنه من إكثار النبي صلى الله عليه وسلم من هذا الدعاء، فأخبره النبي صلى الله عليه وسلم أن القلوبَ بين أُصبعَينِ مِنْ أصابعِ اللهِ يُقَلِّبها كيف يشاء، فالقلب هو محطُّ الإيمان والكفر، وقد سمي القلب قلبًا لكثرة تقلُّبه؛ فهو أَشَدُّ انقِلابًا مِن القِدْرِ إِذا اجتمعَتْ غَلْيًا، فمن شاء الله أقام قلبه على الهدى، وثبته على الدين، ومن شاء الله صرف قلبه عن الهدى إلى الزيغ والضلال.

  • خضوع النبي صلى الله عليه وسلم لربِّه وتضرُّعه إليه، وإرشاد الأمة إلى سؤال ذلك.
  • أهمية الاستقامة والثبات على الدين، وأنَّ العبرة بالخاتمة.
  • العبد لا يستغني عن تثبيت الله له على الإسلام طرفة عين.
  • الحث على الإكثار من هذا الدعاء، تأسِّيًا بالنبي عليه الصلاة والسلام.
  • الثبات على الإسلام هو النعمة العظمى التي ينبغي على العبد أن يسعى إليها ويشكر مولاه عليها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari