Hadisai

Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan neTirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا يَزَالُ البَلاَءُ بِالمُؤْمِنِ وَالمُؤْمِنَةِ فِي نَفْسِهِ وَوَلَدِهِ وَمَالِهِ حَتَّى يَلْقَى اللَّهَ وَمَا عَلَيْهِ خَطِيئَةٌ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa bala'i da jarraba ba zasu gushe ba ga bawa mumini da mumina, a kansa da lafiyarsa da jikinsa, da 'ya'yansa na rashin lafiya ko mutuwa ko sabawa ko wanin haka, haka a dukiyarsa na bukatuwa da tafiya kasuwanci da sata, da tawayar rayuwa da kunci a cikin arziki, har Allah Ya kankare masa dukkanin zunubansa da kurarkuransa da wannan bala'in har idan ya gamu da Allah zai zama ya tsarkaka daga dukkan zunubai da kurakuran da ya aikata.

Fa'idoji

  • Daga cikin rahamar Allah ga bayinSa muminai shi ne ya kankare musu zunubansu a duniyarsu ta hanyar wasu masibu na duniya da aibobinta.
  • Bala'i shi akarankansa yana kankare zunubai da sharaɗin imani, idan bawa ya yi hakuri bai yi fushi ba za'a ba shi lada.
  • Kwaɗaitarwa akan hakuri a dukkan al'amura, cikin abinda yake so da abinda yake ki, ya yi hakuri har ya bada abinda Allah Ya wajabta masa, kuma ya yi hakuri har ya nisanci abinda Allah Ya haramta, yana kwaɗayin ladan Allah, kuma yana tsoron ukubarSa.
  • FaɗinSa: "Da mumini da mumina", karin lafazin mumina a cikinsa akwai dalili akan karin karfafawa ga mace; in ba haka ba da ya ce: "Da mumini" da mace ta shiga cikinsa; domin hakan ba ya kebantar namiji, idan bala'i ya afkawa mace to haka itama an yi mata alkawari da kwatankwacin wannan sakamakon na kankare zunubai da kurakurai.
  • Falalar da ta jerantu akan bala'i tana daga abinda zai sawwakawa bawa abinda yake gamuwa da shi na raɗaɗi akai akai.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم: أن البلاء والاختبار لا ينفكُّ عن العبد المؤمن والمؤمنة، في نفسه من صحتِه وجسدِه، وفي أولاده مِن مرض أو وفاة أو عقوق أو غير ذلك، وفي ماله من افتقار وذهاب تجارة وسرقة، وكَسَادِ عيش وضيق في الرزق، حتى يُكَفِّرَ اللهُ عنه بذلك البلاء كلَّ ذنوبِه وخطاياه حتى إذا لقي الله يكون قد طَهُرَ من كل الذنوب والآثام التي ارتكبها.

  • من رحمة الله بعباده المؤمنين أن يكفِّر عنهم ذنوبَهم في دنياهم بمصائب الدنيا وآفاتها.
  • البلاء بمجرَّده يكفِّر الذنوب بشرط الإيمان، فإذا صبر العبد ولم يسخط أُجِر.
  • الحث على الصبر في جميع الأمور، فيما يحب ويكره، يصبر حتى يؤدي ما أوجب الله، ويصبر حتى يبتعد عما حرم الله، يرجو ثواب الله ويخشى عقابه.
  • قوله: "بالمؤمن والمؤمنة"، زيادة لفظ المؤمنة فيه دليل على مزيد من التأكيد للمرأة؛ وإلا لو قال: "بالمؤمن" لدخل فيه المرأة؛ لأن ذلك لا يختص بالرجل، فإذا وقع البلاء بالمرأة فكذلك هي موعودة بمثل هذا الجزاء بتكفير الذنوب والخطايا.
  • مما يهوِّن على العبد ما يلقاه من الآلام مرة بعد مرة الفضلُ المترتب على البلاء.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari