Hadisai

Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ لَقِيَ اللهَ لَا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا دَخَلَ الْجَنَّةَ، وَمَنْ لَقِيَهُ يُشْرِكُ بِهِ دَخَلَ النَّارَ».

Fassara

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta".

Sharhi

Annabi - tsiara da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa wanda ya mutu ba ya hada Allah da kowa to makaomarsa ita ce Aljanna , koda an azabtar da shi akan sashin zunubansa, kuma cewa wanda ya mutu alhali shi yana tarayya da Allah to zai dawwama a wuta.

Fa'idoji

  • Falalar Tauhidi, kuma cewa shi sababi ne na tsira daga dawwama a wuta.
  • Kusancin Aljanna da wuta ga bawa, kuma cewa shi babu wani abu a tsakaninsa da su sai mutuwa.
  • Gargadi daga shirka, kadan dinta da mai yawanta; domin cewa tsira daga wuta ta hanyar nisantar ta ne.
  • Izina a ayyuka da karshen su ne.
Sharhi: العربية

يُخبرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن مات لا يشرك بالله شيئًا فمصيرُه إلى الجنة وإنْ عُذِّبَ على بعضِ ذنوبِه، وأنَّ مَن مات وهو يشرك بالله شيئًا خُلِّد في النار.

  • فضل التوحيد، وأنه سبب للنجاة من الخلود في النار.
  • قُرْب الجنة والنار من العبد، وأنه ليس بينه وبينهما إلا الموت.
  • التحذير من الشرك قليله وكثيرة؛ لأن النجاة من النار بتَجَنُّبِه.
  • العِبرة في الأعمال بخواتِيمِها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari