Hadisai

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عائشةَ أمِّ المؤْمنِين رضي الله عنها قالت: لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَيْءٍ مِنَ النَّوَافِلِ أَشَدَّ مِنْهُ تَعَاهُدًا عَلَى رَكْعَتَيِ الفَجْرِ.

Fassara

Daga Nana Aisha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr.

Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimta da kuma kiyaye wa ba akan wani abu na nafiloli sama da raka'o'i biyu ratibai na kafin sallar Asuba ba.

Fa'idoji

  • Nafilolin sallah sune waɗanda ba farillai ba na ayyukan ɗa'a, kuma abin nufi a nan: Sunnoni ratibai masu bin farillai.
  • Sunnoni ratibai: Raka'o'i biyu kafin Asuba, da raka'o'i huɗu kafin Azahar da biyu bayanta, da raka'o'i biyu bayan Magariba, da raka'o'i biyu bayan Issha'i.
  • Ana sallatar ratibar Asuba a halin zaman gida da kuma tafiya, saɓanin ratibar Azahar da Magariba da Issha'i, ba a yin su sai a halin zaman gida.
  • An so, so mai ƙarfi a raka'o'i biyun Asuba, saboda haka ba ya kamata a yi sakaci da su.
Sharhi: العربية

أخبرت أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها أن النبي صلى الله عليه وسلم لم يكن على شيء من النوافل أشد تعاهدًا وحرصًا ومحافظة منه على ركعتي الراتبة قبل صلاة الفجر.

  • نوافل الصلاة هي ما سوى الفرائض من الطاعات، والمراد هنا: السنن الرواتب التابعة للفرائض.
  • السنن الرواتب: ركعتان قبل الفجر، وأربع ركعات قبل الظهر واثنتان بعدها، وركعتان بعد المغرب، وركعتان بعد العشاء.
  • راتبة الفجر تصلى في الحضر والسفر، بخلاف راتبة الظهر والمغرب والعشاء فلا تصلى إلا في الحضر.
  • الاستحباب المؤكد في ركعتي الفجر، فلا ينبغي إهمالهما.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari