Hadisai

Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neTirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ رضي الله عنه قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ مَا النَّجَاةُ؟ قَالَ: «امْلِكْ عَلَيْكَ لِسَانَكَ، وَلْيَسَعْكَ بَيْتُكَ، وَابْكِ عَلَى خَطِيئَتِكَ».

Fassara

Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka".

Sharhi

Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sabubban tsirar mumini a duniya da lahira? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Na horeka da al'amura uku: Na farko: Ka kiyaye harshenka daga abinda babu alheri a cikinsa, daga faɗar kowane sharri, kuma kada ka yi wani furuci sai da alheri. Na biyu: Ka lazimci gidanka dan ka bautawa Allah a cikin kaɗaitakarka, ka shagalta da biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ka nisanci fitinu a cikin gidanka. Na uku: Ka yi kuka ka yi nadama ka tuba daga abinda ka aikata na zunubai.

Fa'idoji

  • Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin hanyoyin tsira.
  • Bayanin sabubban tsira a duniya da lahira.
  • Kwaɗaitarwa akan shagaltar mutum da kansa idan ya gajiya daga anfanar waninsa, ko ya ji tsoron cutarwa akan Addininsa da kansa idan ya cakuɗa da mutane.
  • Nuni zuwa himmatuwa da gida musamman ma dai a lokacin fitintinu, shi yana daga hanyoyi dan kiyaye Addini.
Sharhi: العربية

سَأَلَ عُقبةُ بن عامر رضي الله عنه النبيَّ صلى الله عليه وسلم عن أسباب نَجاة المؤمن في الدنيا والآخرة؟ فقال صلى الله عليه وسلم: عليك بثلاثة أمور: الأول: احفظ لسانَك عمّا لا خير فيه، وعن قول كل شر، ولا تنطق إلا بخير. الثاني: الزم بيتَك لِتَعبد الله في الخلوات، واشتغل بطاعة الله عز وجل، واعتزل في بيتك عن الفتن. الثالث: ابْكِ واندَمْ وتُبْ ممّا ارتكبتَ مِن ذنوب.

  • حرص الصحابة رضي الله عنهم على معرفة سُبُل النَّجَاة.
  • بيان أسباب النجاة في الدنيا والآخرة.
  • الحث على انشغال الإنسان بنفسه إذا عَجز عن نَفْع غيره، أو خاف الضرر على دِينه ونفسه إذا خالط الناس.
  • الإشارة إلى الاهتمام بالبيت وخصوصًا عند الفتن، فهو من الوسائل لحفظ الدين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari