Hadisai

Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «يَعْقِدُ الشَّيْطَانُ عَلَى قَافِيَةِ رَأْسِ أَحَدِكُمْ إِذَا هُوَ نَامَ ثَلاَثَ عُقَدٍ يَضْرِبُ كُلَّ عُقْدَةٍ عَلَيْكَ لَيْلٌ طَوِيلٌ، فَارْقُدْ، فَإِنِ اسْتَيْقَظَ فَذَكَرَ اللَّهَ، انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ تَوَضَّأَ انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ صَلَّى انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَأَصْبَحَ نَشِيطًا طَيِّبَ النَّفْسِ، وَإِلَّا أَصْبَحَ خَبِيثَ النَّفْسِ كَسْلاَنَ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci, idan ya farka sai ya ambaci Allah, sai kulli ɗaya ya warware, idan ya yi alwala sai ƙulli ɗaya ya warware, idan ya yi sallah sai ƙulli (ɗaya) ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai, inba haka ba sai ya wayi gari mai mummunar rai mai yawan kasala".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin Shaiɗan da kuma yakinsa ga mutumin da yake nufin tsayuwa dan sallar dare ko Asuba. domin mumini idan ya tafi yin bacci shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙyaraysa - yana nufin: Ƙarshen kansa -. Idan mumini ya farka kuma ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - bai amsa waswasin shaiɗan ba; sai ƙulli (ɗaya) ya warware. Idan ya yi alwala sai ya warware. Idan ya tashi ya yi sallah sai ƙulli na uku ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai; dan farin cikinsa da abinda Allah Ya datar da shi na aikin ɗa'a, yana mai bushara da abinda Allah Ya yi masa alƙawari na lada da gafara, tare da abinda ya gushe daga gare shi na ƙulle-ƙullen Shaiɗan da nauyayawarsa, in ba haka ba zai wayi gari mai mummunan rai, mai baƙin ciki a zuciya, mai kasala daga ayyukan alheri da biyayya; domin cewa shi abin ɗaurewa ne da marin Shaiɗan, kuma abin nisanta daga kusancin Al-Rahman.

Fa'idoji

  • Shaiɗan kowane lokaci yana ƙoƙari ta kowace hanya ga mutum; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, kuma babu tsira ga bawa daga Shaiɗan sai da neman taimakon Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da yin riƙo da sabubban kariya da tsari.
  • Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - da bauta masa suna gadar da nishaɗi a rai da walwalar ƙirji, kuma suna kore kasala da nauyin jiki, kuma suna tafiyar da baƙin ciki da ƙiyayya; domin cewa su suna korar Shaiɗan wannan yana daga wasiwasinsa.
  • Mumini yana farin ciki da datarwar Allah - Maɗaukakin sarki - gare shi dan tsayuwa da ɗa'arSa, kuma yana baƙin ciki dan taƙaitawarsa a matakan falala da kuma cika.
  • Gafala da karkata daga ayyukan biyayya shi yana daga aikin Shaiɗan da kuma kyalkyalinsa.
  • Waɗannan al'amuran guda uku - ambatan Allah, da alwala, da sallah - suna kore Shaiɗan.
  • Ƙullin Shaiɗan akan ƙarshen kai a keɓance; domin nan ce cibiya ta ƙarfi, kuma fagene na jujjuayawrsu, idan ya yi ɗauri akansa sai ya samu damar da zai yi rinjaye akan ran mutum, da kuma jefa barci a kansa.
  • Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Ambatan dare a cikin faɗinsa: "Na horeka da dare", zahirinsa hakan na faruwa ne a baccin dare kadai.
  • Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Babu wani keɓantaccen abu na Zikiri da aka ware akan wannan, da za’a ce wani ba ya wadatarwa sai shi, kawai, dukkan abinda ambatan Allah ya gasgata akansa ya isar, karatun Alƙur'ni yana shiga ciki, da karatun hadisin Annabi, da shagaltuwa da ilimin shari'a, mafi cancantar abinda za'a tinatar da shi faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanda ya farka da daddare sai ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake baShi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya ta tabbata gareShi, Shi Mai iko ne akan dukkan komai, godiya ta tabbata ga Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, babu dabara babu karfi sai ga Allah. Sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini, ko ya yi addu'a za'a amsa masa, idan ya yi alwala za'a karbi sallarsa). Bukharine ya ruwaito shi.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بحال الشيطان وصراعه مع الإنسان الذي يريد القيام لصلاة الليل أو الفجر. فإن المؤمن إذا ذهب إلى النوم يعقد الشيطان على قافيته -يعني: مُؤخَّر رأسه- ثلاث عقد. فإذا استيقظ المؤمن وذكر الله تعالى ولم يستجب لوساوس الشيطان؛ انفكَّت عقدة. فإن توضأ انفكت الأخرى. وإن قام فصلى انفكت العقدة الثالثة، وأصبح نشيطًا طيب النفس؛ لسروره بما وفّقه الله من الطاعة، مستبشرًا بما وعده الله من الثواب والغفران، مع ما زال عنه من عُقَد الشيطان وتثبيطه، وإلا أصبح خبيث النفس، محزون القلب، كسلان عن أعمال الخير والبر؛ لأنه مُقَيَّد بِقَيْد الشيطان، ومُبْعَد عن قُرْبِ الرحمن.

  • الشيطان يسعى دائمًا في كل طريق للإنسان؛ لِيَحُوْلَ بينه وبين طاعة الله عز وجل، ولا نجاة للعبد من الشيطان إلا بالاستعانة بالله عز وجل، والأخذ بأسباب الوقاية والحفظ.
  • ذكر الله تعالى وعبادته تُوْرِث النشاطَ في النفس وانْشِرَاح الصَّدر، وتَطْرد الكَسَل والخُمُول، وتُذْهِب الكَرْب والمَقْت؛ لأنها تطرد الشيطان وهذا مِن وسوسته.
  • المؤمن يُسَرُّ بتوفيق الله تعالى له للقيام بطاعته، ويَكْتَئِب لتقصيره في درجات الفضل والكمال.
  • الغفلة والركون عن الطاعات هو من فعل الشيطان وتزيينه.
  • هذه الأمور الثلاثة -ذكر الله، والوضوء، والصلاة- تطرد الشيطان.
  • العَقْد من الشيطان على مُؤخَّر الرأس خاصة؛ لأنها مَركَز القُوى، ومجال تَصَرُّفِها، فإذا رَبَطَ عليها أمكنه السيطرة على رُوح الانسان، وإلقاء النوم عليه.
  • قال ابن حجر العسقلاني: ذكر الليل في قوله: "عليك ليل"، ظاهره اختصاص ذلك بنوم الليل.
  • قال ابن حجر العسقلاني: لا يتعين للذكر شيء مخصوص لا يجزئ غيره، بل كل ما صدق عليه ذكر الله أجزأ، ويدخل فيه تلاوة القرآن، وقراءة الحديث النبوي، والاشتغال بالعلم الشرعي، وأولى ما يذكر به قول النبي صلى الله عليه وسلم: من تعار من الليل فقال: (لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، الحمد لله، وسبحان الله، ولا إله إلا الله، والله أكبر، ولا حول ولا قوة إلا بالله، ثم قال: اللهم اغفر لي، أو دعا استجيب له، فإن توضأ قُبلت صلاته) رواه البخاري.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari