Hadisai

Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي بَكرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إِذَا الْتَقَى الْمُسْلِمَانِ بِسَيْفَيْهِمَا فَالْقَاتِلُ وَالْمَقْتُولُ فِي النَّارِ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ هَذَا الْقَاتِلُ، فَمَا بَالُ الْمَقْتُولِ؟ قَالَ: «إِنَّهُ كَانَ حَرِيصًا عَلَى قَتْلِ صَاحِبِهِ».

Fassara

Daga Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, kowanne daga cikinsu yana nufin kashe abokinsa, to, mai kisan yana cikin wuta saboda kashe abokinsa, sahabbai suka rikita ga wanda aka kashe; Ta yaya zai zama a wuta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa shi ma yana wuta don kwaɗayinsa a kan kashe ɗan uwansa, babu abin da ya hanashi kisan sai gaggawar mai kisan da kuma rigayarsa da yayi.

Fa'idoji

  • Cancantar ukuba a kan wanda ya yi ƙudiri a kan saɓo da zuciyarsa, kuma ya aikata sabubbansa.
  • Gargaɗi mai tsanani daga rigima tsakanin musulmai, da narko na wuta mai tsanani a kansa.
  • Yaƙi tsakanin musulmai da gaskiya ba ya shiga cikin narkon, misalin yaƙar 'yan tawaye da maɓarnata.
  • Mai aikata babban laifi ba ya kafirta saboda aikata saɓon; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ambaci masu yakin (da) musulmai.
  • Idan musulmai suka haɗu ta kowace sila ce a ka yi yaƙi a cikinta, sai ɗayansu ya kashe ɗayan, to, wanda ya yi kisan da wanda a ka kashe suna cikin wuta, ambaton takobi a cikin hadisin ta hanyar misaltawa ne.
Sharhi: العربية

يُخبر النبي صلى الله عليه وسلم أنه إذا التقى المسلمان بسيفيهما، قاصدًا كلٌّ منهما إتلافَ صاحبِه؛ فالقاتل في النار بسبب مباشرته قتلَ صاحبه، واستشكل الصحابةُ المقتولَ: كيف يكون في النار؟ فأخبر النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه أيضًا في النار لحرصِه على قتلِ صاحبه، ولم يَمنعه من القتلِ إلا مبادرةُ القاتل وسبقِه له.

  • استحقاق العقاب على مَن عَزَمَ على المعصية بقلبه وباشَرَ أسبابَها.
  • التحذير الشديد من اقتتال المسلمين والوعيد عليه بالنار.
  • القتال بين المسلمين بحق لا يَدخل في الوعيد، مثل قتال البُغَاة والمُفسدين.
  • مُرتكب الكبيرة لا يَكْفُرُ بمجرَّد فعلها؛ لأن النبي صلى الله عليه وسلم سمَّى المُتقاتلَينِ مُسلِمَينِ.
  • إذا التقى المسلمان بأيِّ وسيلة يكون بها القتل، فقَتَلَ أحدُهما الآخرَ فالقاتل والمقتول في النار، وذِكْرُ السيفِ في الحديث على سبيل التمثيل.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari