Hadisai

Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي مَرَضِهِ الَّذِي لَمْ يَقُمْ مِنْهُ: «لَعَنَ اللهُ الْيَهُودَ وَالنَّصَارَى، اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ» قَالَتْ: فَلَوْلَا ذَاكَ أُبْرِزَ قَبْرُهُ، غَيْرَ أَنَّهُ خُشِيَ أَنْ يُتَّخَذَ مَسْجِدًا.

Fassara

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce bai tashi daga gareta ba: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai» ta ce; Da badan haka ba da an bayyanar da ƙabarinsa, sai dai cewa an ji tsoron a riƙe shi a matsayin masallaci.

Sharhi

Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce ta tsananta gare shi kuma ya mutu a cikinta: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, Ya koresu daga rahamarSa; hakan domin cewa su sun riƙi ƙaburburan Annabawansu a matsayin masallatai. Ta hanyar yin gini a kansu ko yin sallah a wurinsu ko zuwa garesu (kallonsu). (Nana A'isha) Allah Ya yarda da ita ta ce: Da badan wannan hanin da gargaɗin daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tsoron sahabbai kan abinda za’a yi wa ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar yadda Yahudawa da Nasara suka yi wa ƙaburburan Annabwansu ba da anbayyanar da ƙabarinsa kuma an fito da shi.

Fa'idoji

  • Wannan yana daga wasiyyoyinsa na ƙarshe daga abinda yake nuni akan muhimmancinsu da kuma kulawa da su.
  • Hani mai ƙarfi, da haramci mai tsanani daga riƙon ƙaburbura masallatai, da nufar yin sallah a wurinsu banda sallar jana'iza; to hakan hanya ce zuwa girmama mamacin da kuma ɗawafi a ƙabarinsa da shafa ƙinshiƙansa da kiran sunansa, kuma dukkanin wannan yana daga shirka da kuma hanyoyinta.
  • Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama ƙaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa ga shirka.
  • Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kiyaye Annabinsa - tsira da amincin su tabbata agare shi - da ayi shirka a wurin ƙabarinsa, sai ya cusawa sahabbansa da waɗanda ke bayansu su kiyaye ƙabarinsa da kada a fito da shi.
  • Aikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - da wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kwaɗayinsu akan Tauhidi.
  • Hani daga kamanceceniya da Yahudawa da Nasara, da kuma gini akan ƙaburbura yana daga al'adunsu.
  • Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.
Sharhi: العربية

تخبر عائشة أم المؤمنين رضي الله عنها، أن النبي صلى الله عليه وسلم قال في مرضه الذي اشتد عليه ومات فيه: لَعَنَ اللهُ اليهود والنصارى، وطَرَدَهم من رحمته؛ وذلك لأنهم اتخذوا قبور أنبيائهم مساجد، وذلك بالبناء عليها أو الصلاة عندها أو إليها. ثم قالت رضي الله عنها: ولولا ذلك النهي والتحذير من النبي صلى الله عليه وسلم وخوف الصحابة من أن يُفعل بقبر النبي صلى الله عليه وسلم كما فُعل اليهود والنصارى بقبور أنبيائهم لأُظهر قبره وأبرز.

  • هذا من وصاياه الأخيرة مما يدل على أهميتها والعناية بها.
  • النهي الأكيد، والتحريم الشديد من اتخاذ القبور مساجد، وقصد الصلاة عندها غير صلاة الجنازة؛ فذلك ذريعة إلى تعظيم الميت والطواف بقبره والتمسح بأركانه والنداء باسمه، وكل ذلك من الشرك ووسائله.
  • شدة اهتمام رسول الله صلى الله عليه وسلم واعتنائه بالتوحيد وخوفِه مِن تعظيم القبور؛ لأن ذلك يفضي إلى الشرك.
  • الله تعالى صانَ نبيَّه عليه الصلاة والسلام عن أن يُعْمَلَ الشرك عند قبره، فأَلْهَم أصحابَه ومَن بعدهم، أن يصونوا قبره من أن يبرز.
  • عمل الصحابة رضي الله عنهم بوصية النبي صلى الله عليه وسلم وحرصهم على التوحيد.
  • النهي عن التشبه باليهود والنصارى، وأن البناء على القبور من سننهم.
  • من اتخاذ القبور مساجد الصلاة عندها وإليها، ولو لم يُبْنَ مسجدٌ.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari